Bilicin: Kyau na haƙiƙa ko illa mai ɗorewa?

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

A cikin al’ummarmu ta yau, musamman a tsakanin mata da matasa, canjin launin fata ya zama daya daga cikin fitattun abubuwan da ake nunawa a matsayin wayewa da kyau. Fatar da ta yi fari na da karbuwa, da ɗaukar ido, da kuma tasiri a kafafen sada zumunta. Wannan ne ya sa da yawa a matasa musamman mata suke ganin kyau ba ya taɓa cika ba tare da hasken fata ba. Wannan ne ke kai su ga sha’awa ta sa wasu tunanin neman hasken ta kowace hanya, dalilin da ke kai su ga abinda ake cewa bilicin.

Shafin kwalliya na wannan mako zai yi duba kan ma’ana da kuma illa ko faidar da ke cikin bilicin idan akwai shi. Kafin komai bari mu fara da tambayar ma’anar kalmar bilicin. 

Shin menene bilicin? Ta yaya ake yin sa? Yana da amfani kuwa ko kuwa cuta ce aka lulluɓe da kyakkyawan suna? 

Me ake nufi da bilicin a mahangar masana?

A cewar Dakta Halima Tijjani, ƙwararriya a fannin lafiyar fata a asibitin koyarwa ta Aminu Kano:

 “Bilicin hanya ce ta rage ko kawar da sinadarin melanin daga jikin fata, wanda shi ne ke ba mutum launin fata da kare shi daga rana.”

Bilicin wani nau’in sauya launin fata ne da ke amfani da sinadarai masu ƙarfi da sauyin tsarin halitta. A mafi yawancin lokuta, ana ɗaukar shi da sunan “gyaran fata”, alhali kuwa hakan ya bambanta da kulawa ta lafiya.

Ta yaya ake yin bilicin?

Mutane na amfani da hanyoyi daban-daban wajen yin bilicin, wasu daga cikinsu sun hada da:

Kayan shafawa: Kamar lotions da sabulai masu sinadarai irin su hydroƙuinone, mercury, da steroids.

Allura da kwayoyi: Kamar glutathione injection da wasu capsules da ke hana samar da melanin daga tushe.

Tiyata da laser: Wanda ake yi a cibiyoyi masu suna “spa” ko “beauty clinic”, ba tare da sahalewar likita ba.

Wani bincike da hukumar NAFDAC ta fitar a 2024 ya nuna cewa, kashi 68% na kayan bilicin da ake amfani da su a Najeriya ba su da rajista kuma suna ɗauke da sinadarai masu guba.

By ukarofi