Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Gaskiyar Magana abun da na san a ɗauko wannan darasi don ya na alaƙa da gabar ta tsakiya da batun yanayin siyasar yankin da kuma duniya gaba ɗaya. Kazalika ba zan ɗauko lamuran da su ka shafi tsaro ba a nan don a zahiri ba abun da ake tattaunawa ba kenan kuma duk wasu bayanai da a ka kawo na baya wa imma sun wuce ko masu kawo su na shiga sharo ba shanu. Duk abun day a shafi matakan can baya hasashe ne kawai kuma ni abun da ya ɗau hankali na bayanan Sheikh Ahmad Gumi na cewa matsayar sa kan siyasar duniya kuma mun san abubuwa da ya ke fada da su ka shafi Falasɗinawa ko Gaza. In na taɓo batun na malamin zan koma na duba yadda a ke ƙoƙarin shiga wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita tsakanin Isra’ila da Hamas.
AN TARE SHEIKH AHMAD GUMI DAGA IZININ SHIGA MADINA
Rahotanni sun bayyana cewa an dakatar da malamin Islama a Nijeriya Sheikh Dokta Ahmad Gumi daga shiga Madina don gudanar da aikin hajjin bana.
Gumi dai na daga tawagar malamai da hukumar alhazai NAHCON ta ɗauka don faɗakar da alhazai a lokacin aikin hajjin bana na 2025.
Bayan dawowar sa daga Madina, Dokta Gumi ya ɗora alhakin kin barin sa ya shiga Saudiyya da irin ra’ayoyin sa kan siyasar duniya.
Yayin da ya godewa hukumomin Nijeriya don aniyar bin kadun lamarin, Gumi ya ce yanzu zai samu damar kula da lafiya da gonar sa.
Bayanin na Sheikh Gumi bai wadatar da wasu kafafen labaru ba don sun cigaba da waiwaye su na ɗauko wasu labaru na shekarun baya da su ka yi sanadiyyar riƙe malamin a can Saudiyya kafin ya dawo gida. Masu wannan rubutun ba su tuntubi Saudiyya ko zantawa da malamin don ƙarin bayani ba amma su ka shiga sharhi kawai. Aƙalla ma da an samo bayanai daga ofishin jakadancin Nijeriya a Saudiyya ko ma wasu daga malaman da su ke tare da Sheikh Gumi a lokacin da abun ya faru. Ba mamaki ba don rubutun da malamin ya yi a shafin san a fesbuk ba labarin ma ba zai samu ba ko ma ba lallai kai tsaye a san ya dawo gida ba. Ai da yawa ko ma kakaf in ka ɗebe ‘yan jaridar labarum aikin hajji ba wata kafa da ta ɗau labarin tashin Sheikh daga Kaduna zuwa Madina amma caraf da aka ji ya dawo sai kawai mu ka yi ta ganin sharhi iri-iri. Ni a ɓangare na ba zan ɗorar da wani bayani ba sai an samu bayanai daga hukumomin Nijeriya da Saudiyya. Malamin kan sa ya godewa hukumomin na Nijeriya don bin kadun lamarin. A nan kawai zan bi gefen kwarin kunya ne na yi Magana kan Falasɗinawa da has ashen da malamin ya yin a cewa siyasar duniya ce ko matsayar sa kan siyasar ce ta sa ɗaukar matakin a kan sa. Tabbas malamin zai iya jin wasu bayanai daga wajen jami’ai a nan filin jirgin ko kuma ba mamaki an bad a umurni ne cewa in ya sauka kar a bar shi ya shiga ƙasar. Dokta Gumi ba baƙon Saudiyya ba ne don ma tamkar mazaunin birnin Makkah ne kuma a can ma ya yi karatu mai zurfi. Zan kuma yi ta babban mahaukaci duk duniyar Nijeriya mahaifin sa marigayi Sheikh Abubakar Mahmud na kan gaba a mutanen Afurka da Saudiyya ta karrama. Mu tuna kyautar lambar gida ta Sarki Faisal da a ka ba wa marigayin a 1987. Idan ba wasu dalilai da su ka kawo sabani ba ai Dokta Ahmad da zai zama mai jawo alherai ga Nijeriya daga Saudiyya kama daga tura ɗalibai su yi karatu can, taimakon marayu har ma da iya ba da shawara kan tallafawa al’ummar Gaza ga irin abun da Saudiyya za ta iya yi bias siyasar duniya. Duk mai bin rubutun da na ke yi zai fahimci abun da na ke nufi a nan. Kawo batun alaƙa da yaron nan nan Umar Mutallab da a ka zarga ya dau wani abu da zai iya fasa jirgi duk da hakan bai yi nasara ba wani abu ne daban don Amurka ta ɗau matakan ta a kai kuma hatta mahaifin matashin ya fito karara ya yi bayani da ma sanar da Amurka halin da ɗan nasa ya ke ciki. Masu dogon waiwaye kan wannan batun ba su da gagarumar hujja da ta wuce yanayin aikin jarida mai waiwaye-waiwaye. In ma mun dau ziyarar da Dokta Ahmad ya kai Iran wajen wani taro day a shafi lamarin addini cewa zai iya shiga bakin littafin Saudiyya nan take zan ce sam ba haka ba ne don tun mulkin tsohon shugaban Iran Ibrahim Raisi da ya rasa rai a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu, Saudiyya ta sulhunta da Iran. Ministan wajen Iran wanda shi ma ya na jirgin Hussein Abdollahian ya shiga Saudiyya a ka kulla yarjejeniyar sulhu a ka sake buɗe ofisoshin jakadancin juna a kasashen biyu. Wannan ma haƙiƙa shi ya kawo sauƙi ko dakatar da hare-haren Houthi ta Yaman kan Saudiyya. Zuwa Iran ba zai jawowa Dokta Gumi jakar tsaba batun yau kowa daga Iran kai tsaye zai shiga Saudiyya ya gudanar da aikin hajji. Abu ɗaya ne zan iya cewa za mu iya alaƙantawa nan ma don dalilan sharhi ne da kuma ɗan tsokacin da Dokta Ahmad ya yi kana bun da ya faru wato siyasar duniya. Dokta Ahmad ya fito kwanan nan ya caccaki Saudiyya da yanda ta karɓi baƙuncin shugaban Amurka Donald Trump da ba shi haɗin kai alhali mutan Gaza na cikin uƙuba. Ba Saudiyya ba har da ƙatar da Daular Larabawa da su ka yi goma ta arziki ga Trump amma hakan bai sa sun matsa lamba kan dakatar da yaƙin Gaza ba. Waɗannan bayanai na Dokta Gumi za su iya jawo ma sa jakar tsaba don ƙasashen nan na gudanar da gwamnatocin su ne bias tsarin mulukiyya a gefe guda da Musulunci a ɗaya gefen. Kasancewar su masu mulki irin na gado to lallai su san yadda za su bi da duniya don daulolin su su cigaba da wanzuwa. Marawa Trump baya tamkar kaucewa makircin ƙasashen yamma ne duk da su na danyen ganye da ƙasashen gabar ƙarƙashin ɓladimir Putin na Rasha. Sarkin Larabawa mai fatar ‘ya’yan sa su dore da mulki a bayan rayuwar sa sai ya iya a ciza a hura in ba haka ba a cillo ma sa wata fitina da za ta shafe shi ta kuma shafi tsaro da tattalin arzikin ƙasar ta sa. Mun manta duk da marigayi shugaban Masar Muhammad Morsi mulkin dimokraɗiyya ya kawo shi mulki amma kwana nawa ya yi kan karaga a ka ture shi. Ga marigayi shugaba Saddam Hussein na iraki duk gwagwarmayar sa da jajircewa kan manufofin mulkin sa amma yaya a ka kare. Mu dawo nan Afurka mu duba yadda a ka yi ta gindaya gadar zare ga marigayi shugaban Libya Moammar Gaddafi duk da alherin da ya shuka a Libya. Yaya Sudan bayan mulkin Janar Omar Elbashir kun ga haka a ka yi ta kiki-kaka har a ka tagaiyara kasar. Dokta Ahmad Gumi na da na sa tsari na wa’azi kuma ya na iya yin hakan a Nijeriya don tsarin gwamnatin mu mai ba da dammar daidai gwargwado a faɗi albarkacin baki kuma gwamnatin na saurarawa ‘yan manya ko fitattun gidaje kamar gidan Sheikh Abubakar Mahmud Gumi. Mu sani Larabawa da ke mulkin mulukiyya ba su da jimirin as-as.
Mu leƙa Gaza inda sabon harin sojojin Isra’ila kan Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 46 ciki har da masu samun mafaka a wata makaranta su 31 yayin da su ke barci.
Wannan na daga yunƙurin Isra’ila na kwace dukkan Gaza ya koma ƙarƙashin mulkin ta da ma kwato kamammun Isra’ilawa da ke hannun Hamas.
Tun wargajewar sulhun dakatar da buɗe wuta a Maris, Isra’ila ke cigaba da ruwan boma-bomai kan Gaza da zummar murƙushe Hamas da kaurar da jama’ar yankin su yi gudun hijirar kashin kai.
Hatta batun dawo da tura kayan agaji bai yi wani tasiri ba don yanda ‘yan Gaza ke matuƙar buƙatar magunguna da abinci da a ka datse shigowa da su watanni biyu da rabi da su ka wuce.
Har dai Isra’ila za ta murƙushe Hamas gaba daya to sai ta ƙaurar ko gamawa da dukkan al’ummar zirin mai mutum miliyan 1.2.
Muradin ƙaurar da al’ummar Gaza daga ƙasar su ta gado da Isra’ila ta ɗaura damara ya samu suka da rashin amincewa daga Falasɗinawa da kuma ƙasashen duniya da dama in ban da gwamnatin Amurka don shugaba Trump ne ya fara kawo manufar da sunan samun damar sake gina Gaza.
KAMMALAWA
Majiya ta tabbatar da cewa Hamas da ke mulkin Gaza ta amince da wata sabuwar yarjejeniya ta tsagaita wuta da wakilin Amurka Steve Witkoff ya tsara.
Hamas dai ta samu bayanin Witkoff ta hannun masu shiga tsakani kenan da su ka haɗa da ƙasar Masar da Katar.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Isra’ila ke matakin ƙarshe na gamawa da Hamas ko mamaye Gaza da hakan ya fara tun watan Maris bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta baya ta wargaje.
Sabuwar yarjejeniyar ta tsagaita wuta ta tsawon kwana 70 za ta ba da dama Isra’ila ta samu kamammun ta 10 a rukuni biyu daga Hamas.
A yayin tsagaita wuta na kwana 70 za a cigaba da tattaunawa da tsayawar Amurka don neman cimma sulhu na dindindin.
Kazalika za a samu sako wasu fursnonin Falasɗinawa da Isra’ila ke tsare da su a gidajen yarin ta.
In an duba yarjejeniyar baya, ba lallai ba ne wannan ɗin ma ta dore don burin Isra’ila shi ne murƙushe Hamas kakaf.
