
Daga BELLO A. BABAJI
A ƙoƙarinta na ƙwato kuɗaɗen izinin shigowa daga masu jiragen sama na kansu, Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kwastom (NCS), ta hana aƙalla guda 60 aiki a manyan filayen jiragen sama na Nijeriya.
An ruwaito cewa, an rufe tashoshin ajiyar ire-iren jiragen a filayen jiragen sama na Legas da Abuja.
Saidai masu jiragen, waɗanda suka hada jagororin bankuna da masu kamfanonin mai da sauransu sun fara magiya ga Fadar Shugaban Ƙasa domin a sake musu jiragen nasu.
Wasu daga cikin jiragen da aka dakatar da su aiki kamar yadda jami’an Kwastom da na Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama sun haɗa da; Bombardier BD-700 Global 6000, BD-700 Global 6500, BD-700 Global 7500 da dai sauransu.
An samu wasu rahotanni da ke cewa, mafi yawancin jiragen ba su biya kuɗaɗen harajin shigowa da su Nijeriya ba, lamarin da ya sa Kwastom ta yi hoɓɓasan da nufin sa su biyan kuɗaɗen, waɗanda suka kai biliyoyin nairori a jimillance.
Tun da farko, Kwastom ta kirayi masu jiragen da su je ga hukumomin gwamnati waɗanda daga ciki akwai ita da kanta domin a tantance bututuwan jiragen da manufar gano waɗanda ba su biya kuɗaɗen ba.
A ranar Laraba ne aka ruwaito cewa, Kwastom ta fara hana wasu jirage mallakar kansu da na haɗaka tashi. An fara aikin ne a ranar Litinin ba tare da saƙon ankararwa ba, kamar yadda waɗanda lamarin ya shafa suka bayyana.
Ana ganin cewa, NCS ta yi hakan ne duba da cewa a watan Oktoban 2024, ta ƙara wa’adin wata guda domin bai wa masu jiragen wata damar samun cike sharuɗɗan tantancewa da gwamnati ta tsara musu.
