Salman Khan ya buɗe cibiya don koyar da matasa harkar fim 

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Jarumin da ya shahara a Bollywood, Salman Khan, ya buɗe wata cibiyar horas da jarumai a garin Pune mai suna “Khan Talent Studio”. Cibiyar za ta ɗauki nauyin koyar da matasa masu fasaha, musamman daga karkara da garuruwan da ba su da damar shiga fagen fim.

An buɗe cibiyar ne a ranar 2 ga Yuni, tare da halartar manyan mutane kamar Priyanka Chopra da Aamir Khan. Salman ya ce: “Ina so in ga sabbin fuskoki daga inda babu damar bayyana. Idan muna so mu canja fim, sai mu fara da matasa.”

By ukarofi