Daga AISHA ASAS
Jaruma Deepika Padukone ta samu tabbaci daga Cannes Film Festival cewa, za ta gabatar da fim ɗinta ‘Haske da Duhu’ a gasar 2025. Fim ɗin, wanda ke nuna rikicin tunani da ƙyamar mata masu takara a siyasarsu, ya samu goyon baya daga ƙungiyoyin kare haƙƙin mata a Asiya.
Deepika ta bayyana cewa: “Na jima ina burin yin wani abu da zai tava zuciyar mata a duniya. Wannan fim yana cike da jin ƙai da adalci.” An shirya fim ɗin tare da Vishal Bhardwaj, kuma za a nuna shi a karon farko a watan Oktoba.
