Daga AISHA ASAS
A wata tattaunawa da aka yi da jarumin Hollywood mai shekaru 81, Harrison Ford, a ranar 31 ga Mayu, ya bayyana cewa, yana tunanin yin ritaya daga harkar fim bayan kammala wani sabon aikin sa.
Ford, wanda aka fi sani da rawar sa a fim ɗin ‘Indiana Jones’, ya bayyana cewa, jikinsa na buƙatar hutu, kuma yana jin ya cika burin sa na fina-finai fiye da yadda ya taɓa mafarkin yi. “Na yi fim fiye da ɗari, kuma da yawansu sun taɓo zuciyar mutane. Na gode da hakan,” inji shi.
Ana sa ran fim ɗin sa na ƙarshe mai suna “Flight 36” zai fito a ƙarshen wannan shekara, wanda ke bayyana hatsarin jirgi da ceto na gaske da ya faru a shekarar 1987.
