Yobe: Sojoji sun hallaka jagoran Boko Haram, Malam Jidda da ake nema ruwa-a-jallo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Dakarun sojoji na Atisayen HAƊIN KAI sun yi nasarar hallaka babban kwamandan mayaƙan Boko Haram/ISWAP, Malam Jidda a yankin Ngazalgana na Ƙaramar Hukumar Gujba a Jihar.

Hakan ya faru ne a lokacin da dakarun suka farmaki ƴan ta’addar da agajin ruwan alburusai ta sama.

A sanarwar da mataimakin jami’in riƙon ƙwarya na hulɗa da jama’a na sojojin atisayen, Reuben Kovangiya ya fitar, ya ce Malam Jidda shi ne Ameer ɗin ƙauyukan Ngorgore da Malumtu, wanda ya rasa ransa tare da wasu gungun ƴan ta’adda a yayin farmakin na ranar 9 ga watan Yuni.

Ya kuma ce, an yi ba-takashi a tsakanin dakarun tsaron da mayaƙan ƴan inda aka raunata wasu daga cikinsu, lamarin da ya sa suka tsere da raunuka a jikkunansu.

A Ƙaramar Hukumar Abadam kuwa, jami’in ya ce sojoji sun hallaka ƴan ta’adda da dama da gano wasu gawawwakinsu, da kuma ƙwato muggan makamai.

Ya bayyana hakan a matsayin nasara da dakarun suke samu akan ƴan ta’addar wajen daƙile ayyukansu na ta’addanci da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a shiyyar Arewa ta Gabas.

By Babaji