Ambaliyar Mokwa: Gwamnan Neja ya bada tallafin biliyan N1 da aikin titi na N7bn

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yayin nuna damuwa game da iftila’in ambaliyar ruwan sama da aka yi a Ƙaramar Hukumar Mokwa, Gwamnan Jihar Neja Umaru Bago ya sanar da bada tallafi ga waɗanda abin ya shafa domin rage musu raɗaɗi.

A lokacin da ya kai ziyara a sansanin ƴan gudun hijira a makarantar firamare ta Tiffin Madza, gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta bada tallafin Naira biliyan 1 da tireloli guda 50 na kayan abinci ga jama’ar.

Haka kuma, Bago ya sanar da bada aikin titin Mokwa zuwa Raba da gina sababbin gadoji guda huɗu, waɗanda za su lanƙwame kimanin Naira biliyan 7.

Ya bayyana cewa, ayyukan za su taimaka wajen haɓaka kasuwanci a ƙauyuka da kauce wa aukuwar ambaliya a nan gaba gami da sauƙaƙe zirga-zirga.

Bago ya kuma faɗakar da mazauna akan illar gini a magudanan ruwa, yana mai cewa hakan shi ke taimaka wa ambaliya yin ɓarna mai muni.

Har’ilayau, ya ce an umarci ma’aikatar filaye da ta bada takardar shaidar mallaka ga Gwamnatin Tarayya na sauya wa mutanen da iftila’in ya shafa waje.

By Babaji