Aƙalla mutane bakwai sun rasu a yayin da wani babur ya taka wani abin fashewa da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Lakurawa ne suak dasa a Ƙaramar Hukumar Tangaza dake Jihar Sakkwato.
Lamarin ya faru ne a lokacin da mutanen suke kan hanyar dawowa daga hutun sallah daga ƙauyen Gwabro akan babura, inda ɗaya daga cikinsu ya haye kan abin fashewar.
An ruwaito cewa, ann dasa bon ɗin ne a ƙarƙashin wata bishiyar da jami’an sojoji suke sararawa a inuwarta yayin gudanar da atisayensu.
Wata majiya ta ce maza shida ne suka rasu a nan take, inda ɗaya daga cikin mata biyu da suka samu raunuka ta rasu kwana ɗaya bayan aukuwar lamarin.
A lokacin da ya ke tabbatar da aukuwar iftila’in, mataimaki na musamman ga Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Ghazzali Rakah ya ce waɗanda abin ya shafa ƴan ƙauyen Zurmuku ne, waɗanda suka tsaya hutu a ƙarƙashin bishiyar da aka dasa bom ɗin, lamarin da ya yi sandin iftila’in ya same musu.
Ya ce, yana ganin mayaƙan Lakurawa ne suka dasa bom ɗin duba da cewa akwai sojoji a waje.
Tuni aka aika da tawagar lalata bom daga ofishin rundunar ƴan sanda domin binciken yankin don kauce wa fashewar ƙarin wasu boma-bomai.
A makonni kaɗan da suak gabata ne irin haka ya faru a Ƙaramar Hukumar inda sojoji da dama suak rasa rayukansu.
