Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Raɗɗa, ya bayyana matuƙar alhininsa dangane da rasuwar shugaban ƙaramar hukumar Bakori, Hon. Aminu Ɗan-Hamidu, wanda ya rasu a daren Litinin bayan ya sha fama da rashin lafiya.
An zaɓi Ɗan-Hamidu ne tare da sauran shuwagabannin ƙananan hukumoni 33 a watan Maris na wannan shekara, inda ya shafe watanni uku yana shugabancin ƙaramar hukumar ta Bakori.
A watan Afrilu marigayin ya taɓa yanke jiki ya faɗi a filin wasa na Muhammadu Dikko, inda shi da sauran shugabannin ƙananan hukumoni suka yi rantsuwar kama aiki tare.
Daga nan ne aka garzaya da shi asibiti, inda wata majiya ta ce Ɗan-Hamidu yana fama da ciwon asma.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Raɗɗa, Ibrahim Mohammed ya fitar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin mai biyayya ga jam’iyya, gogaggen ma’aikacin gwamnati, kuma dan siyasa mai kishin ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima cikin gaskiya, tawali’u, da sadaukarwar da ba a saba gani ba.
“Katsina ta yi rashin ɗaya daga cikin ‘ya’yanta masu jajircewa da sadaukar da kai, Hon Hamidu ya kasance mutum ne mai natsuwa wanda ya yi imani da riƙon gaskiya da kuma gudanar da shugabanci na gari, mutuwarsa rashi ce mai zafi ba ga Bakori kaɗai ba, har ma ga ɗaukacin jihar baki ɗaya,” in ji gwamnan.
Sanarwar ta ce Gwamna Raɗɗa a madadin gwamnati da al’ummar Jihar Katsina, na miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin, mutanen Bakori, da kuma ‘ya’yan jam’iyyar APC a faɗin jihar.
