Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya koma Abuja bayan kammala hutun sati biyu a Legas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya koma birnin tarayya Abuja, bayan kammala hutun Babbar Sallah da ya shafe tsawon sati biyu yana yi a Legas.

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da wasu jami’an gwamnati ne suka masa rakiya zuwa filin jiragen sama na Murtala Mohammed dake jihar.

A yayin zuwansa Legas, Shugaba Tinubu ya karɓi bakoncin wasu daga cikin manyan ƙasa a gidansa dake Ikoyi.

Sannan, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da dai sauransu.

By Babaji