An harbe direbobi biyu da ƙone tirelolinsu a Imo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

‘Yan bindiga sun hallaka direbobin tirela a matsayar motoci a garin Ogi dake Ƙaramar Hukumar Okigwe ta Jihar Imo.

Jami’an ƙungiyar ƴan union (NURTW) reshen jihar sun shaida wa manema labarai cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 10:30 na safiyar ranar Asabar.

Shugaban NURTW a Okigwe, Dahiru Musa ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce tuni suka sanar da DPO’n ƴan sanda na Ƙaramar Hukumar.

Ya ce, wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar masu fafutukar kafa yankin Biafara (IPOB) ne suka tare hanyar tare da buɗe musu wuta, inda kuma suke ƙone motocin, waɗanda ke ɗauke da buhunan gari.

Daga lokacin ne jami’an sojoji da ƴan sanda suka ziyarci wajen da abin ya faru, inda aka ɗebe gawawwakin da kai su wani asibiti kana daga bisani suka yi musu jana’iza.

A lokacin da ya ke magana game da al’amarin, kakakin ƴan union na manyan motoci a tashar mota ta Laranto dake Jos, Mahmud Jafaru ya ce tirelolin sun nufi zuwa Fatakwal ne a lokacin da abin ya faru.

Ya bayyana cewa, mutane biyun da aka kashe sune Haruna Muhammad da Adamu Ibrahim.

Sannan ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki mataki wajen magance sake faruwar irin haka a nan gaba duba da yadda ake hallaka direbobi da motocinsu ta irin haka.

By Babaji