Adadin wanda suka rasu sanadiyar bom a Sokoto ya kai takwas

Spread the love

Mutane takwas ne aka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon tashin bam da ya afku a ƙauyen Gwabro, ƙaramar hukumar Tangaza da ke Jihar Sokoto, a lokacin bukukuwan babbar Sallah. Waɗanda suka rasu sun haɗa da mata biyu da suka mutu daga baya saboda raunukan da suka samu a lokacin harin.

Wani mai ba da shawara kan harkokin tsaro a Tangaza, Garzali Raka, ya tabbatar da lamarin tare da bayyana cewa ƙauyen Gwabro ya daɗe yana ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga fiye da shekaru biyar. Ya ce wurin da abin ya faru Ɗorawa na da kusanci da sansanin ‘yan ta’adda na Lakurawa, inda aka riga aka samu wasu na’urorin fashewa a baya da suka kasa tashi saboda zafin rana.

Rundunar ‘yan sandan jihar, ta bakin mai magana da yawunta, ASP Ahmed Rufai, ta ce na’urar fashewar da aka ƙirƙira da hannu (IED) ce ta tashi yayin da wasu mutane ke kan hanyarsu daga Gwabro zuwa Zurmuku, kusa da wani sansanin tsaro da ke ƙarƙashin wani itace.

Yankin Zurmuku ma dai ya daɗe yana fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Wasu mazauna yankin da suka tsallake rijiya da baya sun ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da rana yayin da matasa ke zagayen bikin Sallah daga ƙauye zuwa ƙauye. Sun roƙi gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa don kawar da ‘yan ta’adda da ke addabar ƙauyukan Tangaza da Gudu. Wannan hari ya jefa jama’a cikin fargaba tare da dagula bikin Sallah a yankin.

By ukarofi