PDP za ta gurfanar da Matawalle a gaban kotu bisa zargin ɓata sunan Gwamna Lawal

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara ta yanke shawarar maka ƙaramin ministan tsaro, Honorabul Bello Matawalle a kotu bisa zargin ɓata sunan gwamnan jihar Dauda Lawal.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Halliru Andi wanda ya rabawa manema labarai a Gusau.

Haliru Andi ya ce jam’iyyar PDP ta kammala shirye-shiryen ɗaukar matakin shari’a a kan Matawalle kan kisan gillar da ya yi da kuma ikirarin ɓata suna ga Gwamna Dauda Lawal.

Ya ce, “Kwamitin gudanarawa na jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara (SWC) ƙarƙashin jagorancin Dr. Jamil Jibo Magayaki na duba yiwuwar gurfanar da Honarabul Bello Matawalle a gaban kotu bisa zarginsa da yin ikirarin da ba shi da tushe balle makama ga Gwamna Dauda Lawal.”

“Mun bin diddigin maganganun da Bello Matawalle ya yi akan Gwanan Jihar Zamfara Dauda Lawal kuma muna nazarin hukuncin kotu a kansa”.

“Mun yanke shawarar fara gurfanar da shi a gaban shari’a don kawai mu tunatar da shi iyakarsa a matsayinsa na ƙaramin minista domin ya zamo izna ga sauran ‘yan siyasar jihar masu ƙoƙarin ɓata sunan alumma.”

“In ba haka ba, ta yaya Matawalle zai iya taƙaice zai yi maganganun da basu da tushe balle makama don cin zarafin gwamnatin PDP jihar Kuma mu zura ido.”

Yayi gargaɗin cewa, jam’iyyar PDP ba za ta ƙara lamuntar siyasar ɓata sunan wani ba daga ɓangaren Matawalle na APC.

Andi ya bayyana cewa, sun shirya tsaf domin fafatawa da ɓangaren Bello Matawalle na jam’iyyar APC a jihar.

Ya ce, “Ta yaya wanda ya mayar da kanshi abin dariya zai yi ƙarfin halin nuna yatsansa na zargi ga amintaccen gwamnanmu wanda ba ya barin komi a ƙoƙarinsa na ciyar da jihar gaba?.

A cewar Andi, Matawalle ya ɓarnata tsawon shekaru huɗun da ya yi yana faɗa da cin mutuncin tsaffin gwamnoni irin su Ahmad Sani Yariman Bakura, Mahmuda Aliyu Shinkafi, Abdul-Aziz Yari da kuma abokin takararsa na siyasa, Gwamna Dauda Lawal.

Ya ce, “Abun baƙin cikine a matsayinsa na ƙaramin ministan tsaro wanda ya kamata ya fuskanci yaƙi da ‘yan bindiga, ya shagaltu da yaƙi da Gwamna Dauda Lawal da dattawan Arewa”.

“Matawalle yana ganin kamar shi ne Shugaban Tarayyar Najeriya kuma mu a jam’iyyar mu ta PDP mun yanke shawarar nuna masa iyakarsa ta hanyar kai shi kotun da ta dace domin amsa tuhume-tuhume daban-daban kan wuce gona da iri”. Cewar Halliru Andi.

By ukarofi