Ta’addancin intanet: Kotun ta tasa ƙeyar wasu ’yan Chana zuwa kurkuku

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata kotu a Legas ta yanke wa wasu ‘yan ƙasar Chana 9 hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan yari, bisa samun su da laifin zamba ta intanet da kuma ta’addanci.

Mai shari’a D. E. Osiagor a babbar kotun tarayya da ke Ikoyi ne ya yanke hukuncin.

Wazanda aka ɗaure su ne: Li Dong, Deng Wei ƙiang, Huang Bo, ɗiong Zhen, Lai Rui Feng, Zhao ɗiao Hui, Lui Hai Rong, Lui Gang, da Du Ji Feng.

Sun kasance cikin gungun mutane 792 da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kama a wani samame da ta yi a watan Disamba, 2024.

Hukumar ta EFCC ta ce suna da hannu wajen zuba jari na ƙarya na cryptocurrency da badaƙaloli.

An gurfanar da su a watan Fabrairun 2025 da laifin ƙoƙarin cutar da tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar aikata laifuka ta yanar gizo.

Da farko, sun amsa cewa “ba su da laifi.” Amma a ranar 5 ga Yuni, 2025, sun canja ra’ayi inda suka amsa cewa su masu laifi ne, amma suka roƙi kotu a sassauta musu.

Dangane da haka, lauyan masu shigar da ƙara, Nnaemeka Omewa, ya roƙi kotun da ta yanke musu hukuncin da ya dace.

Daga nan ne alƙalin ya yanke wa kowannen su hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan yari tun daga ranar da aka kama su, wato 10 ga Disamba, 2024.

Haka kuma sai sun biya tarar naira miliyan ɗaya kowanne.

Bayan sun kammala zaman gidan yari, alƙali ya ba da umarnin cewa babban kwanturolan kula da shige da fice ya tabbatar da an mayar da su zuwa ƙasar Chana cikin kwanaki bakwai.

Mai shari’a Osiagor ya kuma ba da umarnin a ba wa gwamnatin Nujeriya wayoyinsu, kwamfutar tafi-da-gidanka, da sauran kayan aikin da aka kwace a hannunsu a lokacin da aka kama su.

By ukarofi