Daga USMAN KAROFI
Ma’aikatar noma da tsaron abinci (FMAFS) ta gayyaci dukkan ma’aikatanta zuwa wani zaman addu’a na musamman domin neman taimakon Allah wajen samun nasara a ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da wadataccen abinci da ci gaban ƙasa. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sashen kula da ma’aikata na ma’aikatar ya fitar a ranar 11 ga Yuni, 2025.
An tsara gudanar da zaman addu’ar a ranar Litinin 16 ga Yuni, 2025, a ɗakin taro dake hedikwatar FMAFS, Area 11, Abuja, daga ƙarfe 12:00 zuwa 12:30 na rana. Taken zaman addu’ar shine: Neman taimakon Ubangiji domin kariya da ci gaban ƙasa.” Sanarwar ta shafi dukkan daraktoci, mataimaka, da sauran ma’aikatan ma’aikatar.
Haka kuma, an buƙaci ma’aikatan da su shigo da azumi a ranakun Litinin 16, 23 da 30 ga Yuni, 2025, domin ƙara tsarkake kai da samun albarka yayin gudanar da addu’ar. Sanarwar ta samu sa hannun Mrs. Adedayo Modupe O., Daraktar kula da ma’aikata.
