Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce dakarun Operation Delta Safe, a cikin watan Mayu, sun gano tare da lalata haramtattun wuraren tace man fetur guda 27.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Markus Kangye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Kangye ya ce, sojojin sun kuma daƙile satar mai da ya kai sama da Naira Miliyan 31.4, da suka haɗa da lita 77,530 na ɗanyen mai, lita 10,340 na Dizal, lita 2,700 na Kalanzir da kuma lita 1,240 na man fetur.
Ya ce sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da injina, bututu, injinan haƙo mai, babura uku, wayoyin hannu, da motoci tara.
“Rundunar ‘Operation Delta Safe’ sun ci gaba da aiki na tsawon lokaci a kan ɓarayin ɗanyen mai da sauran masu aikata laifuka a yankin Neja Delta.
“Bugu da ƙari, sun gano tare da lalata injunan tace mai guda 21, da ramuka 34 na tace mai, jiragen ruwa 13, kwale-kwale guda ɗaya, tankunan ajiya 40, da manyan ganguna guda tara.
“Bugu da ƙari kuma, an kama ɓarayin mai 27 da sauran masu laifi yayin da aka ƙwato makamai da alburusai iri-iri,” inji shi.
Kangye ya ce, sojojin sun kuma gudanar da aikin yaƙi da garkuwa da mutane da aikata laifuka a ranar 1 ga watan Yuni, a ƙaramar hukumar Sapele da ke jihar Delta.
Ya ce, an kama wasu masu aikata laifuka uku yayin da aka kama wasu makamai da alburusai, da wayoyin hannu, kwamfutar tafi-da-gidanka, talabijin, da wata mota a hannunsu a yayin gudanar da aikin.
A wani labari kuma, Hedikwatar Tsaro a ƙarshen mako ta ce dakarun Operation DELTA SAFE sun daƙile satar ɗanyen mai da aka kiyasta kuɗinsu ya haura Naira Biliyan 31 a cikin mako guda.
Rundunar sojin ta kuma ce sojojin sun kuma ceto sama da mutane 60 da aka yi garkuwa da su tare da kashe ‘yan ta’adda da dama.
Daraktan Ayyukan Yaɗa Labarai na Tsaro (DDMO), Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ta mako-mako.
A cewarsa, dakarun Operation DELTA SAFE, da ke da alhakin kare kayayyakin man fetur a yankin Kudu-maso-Kudu, sun daƙile ayyukan tace mai ba bisa ƙa’ida ba. Farashin man fetur da aka kwato ya kai Naira Biliyan 31.4.
Daga cikin kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da lita 77,530 na ɗanyen mai na sata, lita 10,340 na Dizal AGO, lita 2,700 na Kalanzir, da lita 1,240 na mam fetur.
Ya ce sojojin sun gano tare da lalata haramtaccen wuraren tace hanya guda 27 tare da tarwatsa kayan aiki da suka haɗa da tankunan ajiya, jiragen ruwa, da injunan tace mai. An kama mutane 27 da ake zargi, an kuma ƙwato makamai, alburusai, da sauran kayan aiki.
