Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyeson Wike ya yi barazanar rufe ofisoshin jakadancin ƙasashen duniya idan har suka gaza biyan harajin ƙasa.
Hakan na nufin cewa ofisoshin jakadancin ƙasashe 34 na fuskantar barazanar rufewa, bayan matakin da aka ga ministan Abuja ya ɗauka a baya-bayan nan kan hukumomin da ya zarga da ƙin biyan harajin.
Aikin ƙwace filaye da minsitan na Abuja ke yi tun bayan hawan sa kan mulki na daga cikin abubuwan da suka fi tayar da ƙura a cikin ayyukan gwamnatin Tinubu a baya-bayan nan.
Sai dai hukumomin Abuja, babban birnin Nijeriya sun ce mutane da hukumomi da dama sun yi watsi da wannan nauyi da doka ta ɗora musu, inda suke ƙin biyan irin waɗannan kuɗaɗe.
Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya Abuja (FCTA) ta ce ana bin ofisoshin jakadacin ƙasashen waje da ke Nijeriya bashin jimillar kuɗi Naira Tiriliyan 3,662, 196 daga shekarar 2014 zuwa yanzu.
Hukumar Abuja ta ce, ƙasashe 34 ne aka samu da laifin ƙin biyan kuɗaɗen harajin filin.
ƙasashen sun haɗa da; Ghana, Rasha, Thailand, Cote d’Iɓoire, Philippines, Netherlands, Turkiyya, Guinea, Ireland, Zambia, Iraƙ, Uganda, Tanzania, Jamus, Congo, ɓenezuela, Koriya ta Kudu, Trinidad and Tobago, Masar, Chadi, Indiya, Sudan, Kenya, Nijar da Saliyo.
Tun farko a ranar 26 ga watan Mayu ne Ministan Abuja, Nyeson Wike ya bayar da umarnin rufe gine-gine 4,794 wadanda suka gaza biyan harajin fili na aƙalla tsawon shekara 10.
Sai dai shugaban ƙasar Bola Tinubu ya shiga tsakani, inda aka tsawaita wa’adin da kwana 14, wanda ya ƙare a ranar Litini, 9 ga watan Yuni.
Bayan cikar wa’adain da minista Wike ya bayar, batun da ke tayar da ƙura shi ne wane mataki hukumomin Abuja za su ɗauka sannan wane tasiri hakan zai yi ga hulɗar diflomasiyyar Nijeriya da ƙasashen da batun ya shafa?
ɓangarori da dama, ciki har da lauya mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Femi Falana sun yi gargaɗi kan tasirin rufe ofisoshin jakadanci wasu ƙasashe a babban birnin Nijeriya.
Harajin fili wani kuɗi ne da doka ta wajabta wa duk wanda ya mallaki fili ya biya gwamnati, kuma wannan ya haɗa da kowa, har da ofisoshin jakadancin ƙasashen waje da ke Nijeriya ba a tsame su daga sauke wannan nauyin ba.
