Ko mai ‘ulcer’ na iya cin nama?

Spread the love

Tare da CIROMA AMINU ASID

Mutane da dama na tambaya akan cin nama ga mai ‘ulcer’, sai dai bincike ya tabbatar da ba kowane abinci ko nama ne ya kamata mai ‘ulcer’ ya ci ba.

Abinci mai ɗauke da sinadarin ‘fat’ (Red meat) wato jan nama, yana da kyau mai ‘ulcer’ ya guji cin wannan nama da yawa kasancewar jikin mutum na ɗaukar lokaci mai tsawo kafin ya narke sinadarin ‘fat’ (red meat), sannan akwai buƙatar sinadarin ‘acid’ da yawa, idan kuma sinadarin ‘acid’ ya yi yawa zai iya sa ‘ulcer’ ɗin mutum ta motsa.

Soyayyen nama; ba a buƙatar mai rashin lafiyar ‘ulcer’ ya ci soyayyen nama da yawa, domin yana ƙara tayar da ciwon ‘ulcer’. 

Sauran nau’in abincin da ba a so mai ‘ulcer’ ya riƙa ci sun haɗa da;

Soyayyen abinci.

Abinci mai yaji.

Abinci mai yami.

Abinci mai zafi.

Taba sigari.

Shan giya.

ƙarin bayani;

Mu sani, waɗannan abubuwa su ake ce wa ‘predisposing factor’, wato ba su ke kawo ita cutar ba, amma suna tayar da ita ne. 

Cutar ‘ulcer’ na samuwa ne ta hanyar shan maganin rage ciwon jiki da yawa, kamar su Ibuprofen, Diclopenac da sauransu. Bayan haka cutar tana ƙara yaɗuwa a cikin al’umma. Don haka sai a kiyaye.

By ukarofi