Daga JAMIL GULMA a Kebbi
An ƙaddamar da gidauniya don samar da tsaro a garin Gulma da ke ƙaramar hukumar mulki ta Argungu a jihar Kebbi.
Da yake jawabi shugaban kwamitin tsaro na yankin ƙasar Gulma Alhaji Kabiru Gandu Gulma ya ce lokacin da aka ƙaddamar da gidauniyar a shekarar da ta gabata an tara kuɗi 8,000.000 inda daga ciki an kashe 6,954,000.00 yanzu haka akwai 2,100,000.00 a cikin asusun.
A wannan karon ana neman sama da naira milliyan talatin da don sayo kayan aiki na zamani saboda a ƙara inganta tsaro.
Shugaban ‘yan sanda na ƙaramar hukumar mulki ta Argungu Sufurtandan ‘yan sanda Abubakar Iliyasu ya bayyana Ubanƙasar Gulma a matsayin jajirtaccen shugaba wanda ya cancanci a yi koyi da shi saboda a ko da yaushe damuwarsa ba ta wuce ta mutanen sa ba.
Sai dai ya nuna damuwarsa bisa ga yadda waɗansu marasa kishin kai suka mamaye harabar ofishin ‘yan sanda da ke garin na Gulma da gine-gine wanda ya kamata a ce akwai wadataccen fili da za a iya ƙara faɗaɗa ta.
Ya bayyana cewa a shirye ya ke a ko da yaushe a ka kira shi wajen wani aiki a duk lokacin da hakan ta taso, inda ya ce ya kamata su ma ‘yan sa kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro da su gudanar da ayyukan su tsakaninsu da Allah.
Da yake jawabi a wajen taron Ubanƙasar Gulma Alhaji Muhammad Bashar Khalid ya ce ya zama wajibi ga kowace al’umma da ta tashi tsaye ta ga ta samar wa kan ta tsaro saboda shi aikin samar da tsaro ba na gwamnati kaɗai ba ne duk da ya ke gwamnatin tana iya ƙoƙarin ta amma dai kowane mutum yana da irin gudummawar da ya ke iya bayarwa musamman a irin wannan lokacin da a ke ciki.
Ya kuma yaba wa Gwamna Malam Nasir Idris bisa ga irin ƙoƙarin da ya ke yi na ɗaukar ƙwararan matakai ba tare da ƙasa a gwiwa ba a duk lokacin da ya samu wani labarin da ya shafi tsaro, haka-zalika mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera bisa ga shawarwarin da ya ke ba su musamman dangane da tsaro.
Ya kuma yaba wa jajirtattun mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu don ganin tsaro ya inganta a garin Gulma waɗanda a lokacin da mutane su ke kwance a gidajensu su kuma suka hana idanuwansu bacci don hana ɓata-gari samun sakewa.
Bayan kammala taron dai an samu kuɗi da naira miliyan goma sha biyar da ya kai haɗi da alƙawurra.
Garin Gulma dai ya samu farmakin ɓarayi da masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa sau uku a baya.
