Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Namadi Sambo ya ƙaryata ikirarin da tsohon Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare na ƙasa, Dokta Shamsudeen Usman ya yi kan batun yi wa wutar lantarki riƙon sukainar kashi a shekarar 2013.
A wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren sa na musamman, Yinka Ibrahim, a Kaduna, ranar Talata, Sambo ya bayyana zargin a matsayin “ƙarya, yaudara, da munafurci,” yana mai cewa an yi su ne domin ɓata sunan gwamnatin Goodluck Jonathan da kuma hukumar kula da harkokin kasuwanci ta ƙasa.
Idan dai ba a manta ba, a mulkin Jonathan tsohon mataimakin shugaban ƙasar shi ne shugaban majalisar kula da harkokin kasuwanci ta ƙasa kuma shi ne ya kula da yadda ake sayar da wutar lantarki ga kamfanonin rarrabawa da samar da wutar lantarki.
Usman, a wani taron baya-bayan nan da aka gudanar a Abuja, ya yi zargin cewa tsarin mayar da ɓangaren wutar lantarkin na shekarar 2013 ya kasance ne bisa muradun siyasa, maimakon ƙarfin fasaha
Tsohuwar ministan ta kuma yi ikirarin cewa jiga-jigan siyasa da jami’an gwamnatin Jonathan sun yi kaca-kaca da kamfanonin samar da wutar lantarki.
Duk da rabawa da kamfanoni masu zaman kansu a shekarar 2013, ƙasar ta yi ƙoƙarin ganin an samu ci gaba da aka yi alƙawarin samar da wutar lantarki, inda wutar lantarkin ke ci gaba da lalacewa da kuma fama da rugujewar tsari akai-akai.
Sambo, ya yi watsi da ikirarin Usman a matsayin marar tushe, inda ya bayyana cewa ba shi da masaniya kan duk wani hukunci da ya kawo cikas ga amincin tsarin.
Ya ce, “hankalina ya karkata ga wata magana mai ban mamaki da Dakta Usman ya yi, wanda ke nuni da cewa la’akarin siyasa ya yi tasiri wajen zaɓar waɗanda aka fi so a lokacin da ake tafiyar da harkokin kasuwanci, wannan abin ba’a ne kuma cikakken ƙarya ne.
Sambo ya jadadda cewa, tsarin bayar da kamfanoni ya kasance a bayyane, inda hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa kamar EFCC da ICCP da sauran hukumomin da ke da alaƙa da cin hanci da rashawa suka haɗa da mambobin majalisar.
Sambo ya ce, “A matsayina na shugaban hukumar samar da kamfanoni, na gudanar da ayyukan ne bisa ƙa’idojin da aka kafa da kuma maslahar al’umma, wanda al’ummomin gida da waje suka amince da su.
“A rubuce yake cewa ministan wutar lantarki a lokacin ya yi murabus saboda rashin jituwar da ake samu a harkar sayar da lantarki ga ‘yan kasuwa.”
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ƙalubalanci Dr Usman da ya bayar da cikakkun bayanai game da wasan kwaikwayo da ake zargin wasu mutane ko ƙungiyoyi sun yi a ɓangaren.
Ya ƙara da yin tambaya kan lokaci da kuma dalilin da ya sa Usman ya yi wannan tsokaci, inda ya bayyana cewa tsohon ministan yana da hannu dumu-dumu a harkar hada-hadar kasuwanci da kuma shugabancin kwamitoci da dama.
