Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijetiya, ta hannun Hukumar da ke Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki da Abokan Hulɗa ta ƙasa (FCCPC), ta kai samame ofishin ‘Contact Tele-Performance Company’ (TLC) da ke Abuja, wata cibiyar bayar da biza, inda da rufe harabar cibiyar bayan zargin keta haƙƙin abokan hulɗa da kuma cin zarafin jami’an tsaro da ake zargin jami’an cibiyar da aikatawa.
Daraktar Sa Ido da Bincike ta Hukumar, Misis Boladale Adeyinka, wacce ta jagoranci rundunar jami’an ’yan sandan zuwa harabar ofishin, ta bayyana cewa hukumar ba ta da wani zaɓi illa rufe ofisoshin sakamakon waɗannan laifuffuka.
Ta kuma yi zargin cewa wasu jami’an ofishin sun ci zarafin jami’an tsaron FCCPC.
Adeyinka ta ci gaba da bayanin cewa, an fara binciken kamfanin TLS mai zaman kansa da ke ba da tallafin biza ga ’yan Nijeriya ne a watan Maris ɗin 2025, biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da abokan hulɗa suka yi kan rashin samar da ayyukan da suka biya.
A ranar 25 ga Maris, FCCPC ta ba wa TLS wasiƙa daidai da tsarin warware ƙorafe-ƙorafe. Maimakon su magance koken, jami’ansu sun ci zarafin jami’an FCCPC da ke gudanar da aikinsu na tabbatar da haƙƙin abokan hulɗa.
Ta kuma ƙara da cewa, lamarin ya ƙara dagulewa yayin da jami’an TLS ba wai kawai sun ƙi karɓar takardar sammaci ba ne a gaban hukumar, a’a sun kuma ci zarafin ‘yan sandan da ke ba da tsaro bisa ƙa’ida ga ayyukan FCCPC.
Jami’iyar ta FCCPC ta ci gaba da cewa, “A daidai da sashe na 18(1) (f) na dokar ƙasa da ƙasa ta tarayya, mataimakin shugaban hukumar, Tunji Bello ya bada umarnin rufe harabar.
Ta nanata cewa hukumar tana da dalilai masu yawa da ke nuna cewa wasu ayyukan da TLS ke yi suna lahani ga jin daɗin abokan hulɗa, don haka, an dakatar da ayyukanta har sai an kammala bincike.
A cewarta, an gayyaci manyan jami’an TLS da suka haɗa da manajan ƙasar da manajan cibiyar da su bayyana a gaban hukumar da ƙarfe 2:00 na rana a ranar Juma’a 20 ga watan Yuni, 2025, don bayyana ra’ayin su da kuma kare ayyukan kamfanin.
Adeyinka ta ja kunnen mahukuntan kamfanin kan ƙin amincewa da sabon sammacin da aka yi musu, inda ta ce mummunan sakamako yana jiran waɗanda suka zaɓi ƙin aiwatar da hakan.
Ta ce, “Sashe na 33 (3) na dokar FCCPC ya nuna cewa rashin bin sammaci, ba tare da isasshen dalili ba, laifi ne da zai iya yanke hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari, ko tarar har zuwa Naira Miliyan 20, ko kuma duka biyun.
“Sashe na 33 (4) ya ci gaba da bayyana cewa duk mutumin da ya hana ko kuma ya katse shari’ar Hukumar da gangan yana da alhakin hukunci iri ɗaya. Ayyukan TLS a fili suna ƙarƙashin waɗannan dokoki.”
Ta sake jaddada ƙudirin hukumar na kare masu abokan hulɗar kasuwanci a cikin iyakokin dokar da ta kafa ta hukumar.
