Yadda tsofaffin Ciyamomi biyu suka rasu a lokaci guda a Kano 

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

Alhaji Mahmud Sani Madakin Gini, wanda ake wa laƙabi da Buharin Dala, ya rasu ne a safiyar Litinin da ta gabata sakamakon hatsarin mota a hanyarsa ta dawowa daga Abuja.

Sannan aka yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin a gidansa da ke unguwar Yalwa ta ƙaramar hukumar Dala dake jihar Kano.

Ana tsaka da jana’izar Marigayi Mahmud Sani Madakin Gini ne shi ma tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Wudil shi ma  Alh. Abubakar Abdullahi Likita ya rasu a yammacin ranar. 

Rahoton sun tabbatar da cewa Marigayin ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da jana’izar babban  abokin nasa. 

Tsohon ɗan takarar Gwamnan Kano a zaɓen  shekarar 2032 Dr. Nasiru Gawuna da Hon. Surajo Imam Dala da wasu daga cikin Jigajigan ‘yan siyasa su ne suka kasance tare da mamacin kafin rasuwarsa.

Inda aka yi jana’izar sa a washegarin Talata da misalin ƙarfe 10:00 na safe a gidansa dake Unguwar Bompai da ke cikin birnin Kano.

By ukarofi