2027: Sai bayan babban taron APC Tinubu zai zaɓi abokin tafiya, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yayin babban taron jam’iyyar APC na shekarar 2026 ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai zaɓi abokin tafiyarsa a babban zaɓen 2027 da ke tafe.

Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce, sai an ayyana ɗan takara a hukumance daga jam’iyya kafin a yi maganar zaɓar wanda zai zame masa mataimaki, inda ya ce ba a tare ake faɗar su ba.

Onanuga ya kuma ce, irin haka ne ya faru a lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a lokacinda ya nemi tsayawa takara a karo na biyu.

Ya ƙara da cewa, da zarar Hukumar zaɓe, INEC ta fitar da jaddawalin lokacin gudanar da zaɓukan 2027, za a yi babban taron jam’iyya wanda daga nan zai zaɓi abokin tafiyarsa.

Har’ilayau, game da ikirarin kasancewar Tinubu a lokacin da ya ke gwamnan Legas ya canza mataimaki har sau biyu, hakan ya nuna cewa akwai shirin canza Shettima, lamarin da Onanuga ya ce jita-jita ce mara asali domin kuwa bai san wani rikici a tsakaninsu ba.

Akan haka ne Onanuga ya kara da cewa, idan ma za ayi la’akari da sauyin mataimaki da Tinubu ya yi a yayin jagorancin Legas, kuma sai a yi nazari game da rikicin da ya shiga tsakaninsa da su, yana mai cewa har yanzu akwai girmamawa da kyakkyawar alaƙa a tsakanin Shettima da mai gidan nasa.

By Babaji