Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin shugaban ‘yan sandan ƙasar Kenya ya ajiye muƙaminsa domin bada damar yin binciken mutuwar marubuci ɗan gwagwarmayar ƙasar Albert Ojwang da ya mutu a hannun ‘yan sanda a ƙasar.
Biyo bayan matsin lamba daga ƙungiyoyi da kuma jama’ar ƙasar da ta kai ga yin zanga-zanga har da lalata kaddarori, inda suka buƙaci gwamnatin Kenya da ta bi haƙƙin Marigayi Albert Ojwang, mataimakin ‘yan sandan Kenya Eliud Langat ya sauka daga muƙaminsa tare da alƙawarin bada dukkan goyon bayan da za a buƙata yayin bincike.
Rfi ta rawaito cewa a cewar shugaban ‘yan sandan Kenya Douglas Kanja ya ce murabus ɗin mataimakin nasa za ta bada damar yin sahihin bincike ba tare da ganin ido ko yin alfarma ba.
Jami’an tsaron ƙasar sun kama Marigayi Ojwang ne a ranar 7 ga watan Yunin wannan shekara 2025, bisa zargin cin mutunci da yaɗa rahotanin ƙarya kan mataimakin babban jami’in ‘yan sandan ƙasar a shafukansa na sada zumunta.
Albert Ojwang ya rasa ransa a ranar 8 ga wannan watan kwana ɗaya da kama shi a wani asibitin ƙasar, lamarin da ya tayar da hankulan jama’a.
‘Yan sanda a Kenya sun yi ƙaurin suna wajen cin mutuncin matasa dake sukar lamirin gwanmnatin Shugaba Ruto, sai dai mutuwar Ojwang ya tunzura jama’ar ƙasar har ta kai su ga kira ga Shugaba Ruto da ya yi murabus.
