Gwamnatin Tarayya za ta ƙwace lasisin haƙo mai daga kamfanonin da ba sa kataɓus

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar da ke Sa Ido Kan Harkokin Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC), ta shaida wa masu samar da man fetur cewa ta shirya aiwatar da manufar ‘A haƙo ko a janye’.

Shugaban Hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe, ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar Masu Sarrafa Man Fetur Mai Zaman Kanta a hedikwatar hukumar da ke Abuja kwanan nan.

A cewar wata sanarwa da NUPRC ta fitar, Komolafe ya jaddada cewa dole ne masu samar da mai da iskar gas su fara haƙowa cikin ƙayyadadden lokaci ko kuma su ajiye lasisin su. 

Ya bayyana cewa manufar tana da nufin farfaɗo da fannin mai, da tabbatar da yin amfani da kadarorin da ya dace, da kuma bunƙasa kuɗaɗen shiga na gwamnati.

“Komolafe ya kuma tattauna yadda za a aiwatar da manufar ‘a yi aiki ko a ajiye’, wanda ke buƙatar masu gudanar da aiki ko dai su fara aiki tuƙuru a cikin ƙayyadadden lokaci ko kuma su ajiye lasisin su. Wannan manufar na da nufin farfaɗo da fannin mai, tabbatar da yin amfani da kadarorin da ya dace, da kuma bunƙasa kuɗaɗen shiga na gwamnati,” inji babban jami’in NUPRC.

Economic Confidential ta ruwaito cewa ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur Heineken Lokpobiri, ya sha alwashin aiwatar da manufar ‘a haƙo ko a janye’, yana mai cewa gwamnati za ta karɓe dukkan rijiyoyin man da ba sa aiki daga hannun masu aikin da ke riƙe da su.

A halin da ake ciki, a wajen taron, Komolafe ya yi maraba da tawagar tare da jaddada aniyar NUPRC na samar da yanayin kasuwanci.

Ya zayyana wasu muhimman tsare-tsare da aka aiwatar tun lokacin da aka kafa dokar masana’antar man fetur, da suka haɗa da sarrafa ƙa’idoji kamar ba da lasisi da izini, wanda ya ce sun rage jinkirin aiki da kuma inganta ayyukan aiki a sassan.

Sanarwar ta bayyana cewa, tawagar ta samu jagorancin shugaban ƙungiyar IPPG, Abdulrazaƙ Isa, wanda kuma ke riƙe da muƙamin shugaban ƙungiyar Waltersmith, wani kamfanin mai da iskar gas.

By ukarofi