

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Laftanal Kafayata Omolara, wadda ita ce mace ta farko a rundunar sojojin sama ta Nijeriya da ta zama matuƙiyar jirgin yaƙi, ta sake zama gwarzuwar ɗaliba a Kwalejin Horar da Sojoji ta Ghana (GAFCSC), inda kuma ta samu babbar kyauta ta ‘Best Assistant Commandant Paper’.
An gudanar da taron karramawar ne a Accra, Babban Birnin ƙasar.
Jami’ar ta samu kyautar ne a sakamakon nuna ƙwarewa da jajircewa a yayin zamanta a GAFCSC.

A sanarwar da rundunar sojojin sama ta fitar, ta ce nasarar da jami’ar ta samu ya nuna yadda jagorancin Nijeriya a harkar tsaron shiyya ke ƙara ƙarfi da damawa da mata a harkar sojoji.
A shekarar 2019 ne aka gabatar da ita a matsayin soja mace ta farko da ta ƙware a fannin tuƙin jirgin yaƙi bayan kammala karatunta a Amurka.
Tun daga lokacin ne ta cigaba da ɗaukar horo a matakan fannin da dama da bada horo ga matuƙa jirgin sama na sojoji masu tasowa.

