Daga HABU ƊAN SARKI a Jos
Wasu matafiya 12 da suka fito daga yankin Basawa dake ƙaramar hukumar Zariya a Jihar Kaduna sun gamu da ajalinsu sakamakon kisan gilla da wasu matasa suka far musu a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure a yankin ƙaramar hukumar Qua’an-Pan.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya auku ne a daren Jumma’a da ta gabata, a tsakanin yankin Mushere da Chakfem da ke ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa mutum 11 daga cikin matafiyan suna samun kulawa a asibiti, bayan raunukan da suka samu a harin da aka kai musu, ciki har da mata da ƙananan yara.
Ayarin ‘yan ɗaurin auren su 31 sun tafi bikin ne cikin wata bas mallakin Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta Zariya, wacce ƙauyawan da suka far musu suka kashe direban motar da wasu daga cikin matafiya tare da ƙona motar ƙurmus.
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a harin, Ibrahim Umar, ya ce, “Mun kusa kaiwa Qua’an-Pan bikin ɗaurin auren ɗan’uwanmu, amma muka yi ɓatan kai saboda ba mu san hanyar ba. Mun tsaya tambayar wasu mutane kwatance, kafin mu farga har sun yi mana ƙawanya sun zagaye motar ta kowace kusurwa, suna ihu cewa a kashe mu, mu Hausawa ne. Daga nan suka fara duka suna kawo mana hari da muggan makamai.
Ya ƙara da cewa, daga waɗanda aka kashe har da mahaifin angon da za a je ɗaurin auren sa, ƙaninsa da kuma yayansa.
Babban Limamin Masallacin Jumma’a na Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), da ke Mangu, Sheikh Suleiman Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa an ajiye gawarwakin a Babban Asibitin Mangu.
Sheikh Suleiman Haruna, ya ce, “Matafiya 31 ne a motar. Mun samu gawarwakin mutum takwas, amma mun roƙi jami’an tsaro su taimaka wajen kawo ragowar gawarwaki huɗu da suka rage. Muna tare da shugaban ƙaramar hukumar Mangu kuma yana iya bakin ƙoƙarinsa a kan lamarin.”
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang tare da Kwamishinan ýan sanda na jihar da wasu ƙusoshin gwamnatin Filato da suka yi wa Gwamnan rakiya, sun ziyarci wajen da lamarin ya auku, da babban asibitin Mangu, inda sauran matafiyan da suka jikkata ke samun kulawar likitoci.
Ya yi Allah wadai da aukuwar lamarin abin da ya kira ɗanyen kai da rashin hankali, tare da jajentawa Masarautar Zazzau da Gwamnatin Jihar Kaduna, bisa wannan kisan gilla, wanda ya ce ya auku ne a yayin da jama’ar Mangu da Bokkos ke cikin alhinin hare-hare da asarar rayukan ýan’uwansu da suke yi daga ýan ta’adda.
Ya buƙaci jami’an tsaro su tabbatar da ganin an kawo ƙarshen hare-haren da yake addabar yankin, da gano masu haddasa shi.
A cewarsa, “Kada wannan al’amari da ya faru ya sa matafiya ƙauracewa hanyoyin Jihar Filato, jami’an tsaro za su cigaba da ba su kariya, har su isa inda za su sauka cikin kwanciyar hankali.”
Tuni Gwamnan ya kira takwaransa na Jihar Kaduna a waya ya jajenta masa game da al’amarin, yayin da ya aika da tawaga ta musamman don yin ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka gamu da, wannan ibtila’i, masarautar Zazzau da gwamnatin Jihar Kaduna.


