Yasassun kalamai cikin wa’azozi da illolinsu ga tsaro

Spread the love

Daga HASSAN IMRAN

Malamai su ne magadan Annabawa. Allah Ya basu haƙƙin ilimantar da al’umma akan sha’anin addini da kuma dukkan harkokin rayuwa. Musulunci, addini ne da Ya yi mana bayani kan yadda za mu gudanar da harkokin rayuwarmu, kamar harkokin kasuwanci, siyasa, tattalin arziƙi, zamantakewa da sauran buƙatun rayuwa.

Bisa ga haka, magabata na ƙwarai suka jajirce wajen ilimantar da al’umma da kuma rubuce-rubuce akan waɗannan fannoni na rayuwa. Sun bi turbar Annabawa wajen karantar da al’umma ba tare da kawo son rai a karantarwarsu ko kuma kawo saɓani a cikin al’umma ba. Wannan ya haifar masu da kima da mutunci a idanun mabiyansu da sauran al’umma. Sun kasance suna wa’azi da nasiha cikin hikima da kyawawan kalamai yadda Alƙur’ani da hadisin Ma’aiki (SAWA) suka karantar da mu.

Wannan ba yana nufin cewa ba sa samun saɓanin fahimta ba ne, amma ba sa barin hakan ya janyo hargitsi ko kuwa cusa ƙiyayya a zukatansu ko na mabiyan su. Wannan ya ƙarfafa masu zaman lafiya mai ɗorewa, kuma ya kawo masu cigaba mai ƙarfin gaske.

Abin takaici da ban haushi shi ne yadda muka wayi gari a yau, harkar malanta ta zama abin wasa da kowa yana cusa baki a cikinta ba tare da wani ƙwaƙƙwaran ilimi ba. Sai ka samu wanda ko karatun Fatiha bai iya ba, amma saboda ya iya turanci ko yana tinƙaho da ya san Ahadari ko kuma ya yi bincike ta na’ura mai ƙwaƙwalwa akan wani batun addini da bai san sahihanci shi ba, sai ya shiga shafukan sada zumunta ya yi ta rubuce-rubuce; yana nuna cewa shi ma ya zama malamin da ya isa ya bada fatawa akan harkokin addini. 

Masu hikima na cewa ƙaramin sani ƙuƙumi ne. Harwayau, akwai wasu malaman addinin da babu wa’azin ko nasihar da za su yi ba tare da sun yi zagi ko cin mutuncin wasu ba. Ko su soki wata ƙungiyar da fahimtarsu ta bambanta da tasu.

Haka zalika, wasu na kafurtar da mutane babu gaira babu dalilli akan wani ƙaramin al’amarin addini da bai taka kara ya karya ba. Su kafurtar da wanda suka so kuma su musuluntar da wanda suka so.   Ire-iren waɗannan yasassun wa’azozin ne  suke janyo cece-kuce, da rikice-rikice a tsakanin mabiya addini, da ta ke haifar da munanan yakukuwa. 

A wannan zamani da muke ciki saboda yawaita shafukan sada zumunta, waɗannan malamai masu ra’ayin rikau sun koma kan shafukan zumunta suna yada munanar fahimtar su mai kama da ra’ayoyi irin na ‘yanta’adda a mafi yawan lokuta. Na ci karo da wani saƙon da wani malamin addinin ya wallafa a shafinsa ta manhajar Fezbuk yana cewa, “Wato wasu malamai da daliban ilimi basusan haɗarin isbali da aske gemu ba. Ko wallahi duk malamin da yake aske gemu kuma yana isbali, bai cancanci ya zama limamin Jumma’a ba, ko shugabancin mutane, don mai yin hakan fasiƙi ne.” Allah Ya shiryar da mu. Irin waɗannan maganganun ne ke cusa ƙiyayya a zukatan mabiya da rura ra’ayin ta’addanci, idan hukuma bata ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki ba.

Jahilci da rashin hikima wajen wa’azi shi ya janyo rikicin Maitatsine a garin Kano a shekara ta 1980. Maitatsine, Wanda asalin sunansa shi ne, Muhammad Marwa, da mabiyansa suna wa’azin da yake janyo ruɗani da hargitsi a cikin harkokin addini. Suna gudanar da harkokin addini ta hanyoyin da suka saɓa wa ainihin karantarwa addinin Musulunci saboda jahilci. Wannan ya saka wasu jihohi a Arewa suka kafa dokar ta zata magance iri-iren waɗannan mumunan wa’azizuka domin magance faruwa wannan rikicin a gaba. Haka zalika, rikicin yan ta’addan Boko Haram da Lakurawa duk ta samo asali ne wajen zazzafi wa’azi da kuma muguwar ra’ayin aƙidda da kuskuran fahimtar addini. Har wayau, muna kam fama da ta’addacin kungiyar Boko Haram da kuma ta Lakurawa. Suna garkuwa da mutane kuma suna kashe mutane babu gyara babu dalili.

Asalin abinda yake janyo wa waɗannan matsaloli na yasassun wa’azozi shi ne rashin dokar da za ta tantance waɗanda suka dace su yi wa’azi da kuma basu lasinsin haka. A shekarar 2016 Gwamnatin Jihar Kaduna a ƙarƙashin Malam Nasir El-Rufa’i ta tura wata doka Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna, domin magance irin waɗannan yasassun wa’azozi. Jigo a wannan dokar shi ne domin bunƙasa zaman lafiya da kyautata zaman tare a tsakanin al’umma, da kuma daƙile kowacce rikici ta addini. Gwamnan ya yi bayanin cewa ba hana wa’azi yake so ya yi ba, amma yana so ne ya kawo dokar da za ta tsaftace wa’azozi da masu wa’azi. Abin mamaki mabiyan addinin Islama da Kiristoci da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam suka caccaki wannan dokar. Wannan ya sanya dokar bata haifar da ɗa mai ido ba.

Abin sani ne cewa inda ba a ƙayyade irin wa’azin da ya dace a yi ba kuma aka bar jahilan malamai suna cin karensu babu babbaka to, tabbas za su kawo matsalolin ga addini da kuma ainihin karantarwar sa. Sayyidina Umar bn Abdul’Aziz (Allah Ya yi masa rahama) ya ce, ‘Duk wanda ya yi wa Allah hiddima (ta bauta ko bunƙasa addininsa) ba tare da ilimi ba zai tabka ɓarna sosai fiye da ayyukan alkhairi.’ 

Sau da yawa, jahilci da rashin fahimtar asalin karatun addini shi ke haifar da ra’ayin riƙau akan addini da zazzafar aƙida da gagararru, kangararru da kuma masu ta’addanci da sunan addini suke imani da shi. 

Sananen abu ne cewa babu inda Musulunci ya karantar da ta’addaci ko tada tarzoma da sunan addini. Shi Musulunci addini ne tsaka-tsaki. Wasu mutane uku sun zo gidan matan ma’aiki Sallallahu alaihi Wasallama domin tambaye irin ayyukan alkhairi da Manzon Allah ya kasance yana aikata wa.

Da suka sanar da su a irin ayyukansa, sai suka raina ayyukan nasu suka ce: A ina mahadin mu da wanda aka gafarta masa zunubansa na baya da na baɗi. Sai wani a cikin su ya ce: Ni kam, na yanke ma kai na shawara daga yau sallar dare zan duƙufa akai (bani ba bacci kuma). Na biyun su ya ce: Ni ma kam, daga yau zan duƙufa da azumi ba zan yi buɗa baki ba. Na ukun su shi ma ya ce: zan ƙaurace wa mata, ba zan yi aure ba (har abada).

Da Manzon Allah ya dawo ya ji batun waɗannan mutane sai ya fuskance su ya ce: shin ku ne waɗanda kuka ce haka da haka? Amma wallahi ku sani cewa na fi ku tsoron Allah kuma na fi ku kiyaye dokokin sa; ina azumi kuma ina buɗe baki,  ina bacci kuma ina tsayuwar dare kuma ina auren mata. Saboda haka duk wanda ya ƙauracewa tafarkina ko koyarwata (Sunnah) to, baya tare da ni. Mu gan yanda Manzon Allah ya shirye da waɗannan mutanen da suka so su wuce gona da iri da sunan ibada ga Allah.

Haka zalika, babu sashi na rayuwa ɗan Adam da babu wata dokar da take shiryar da mutane akan al’amarin rayuwa ko dokar Allah ko kuwa kundin dokar bil adama.

Hanyoyin da za a magance waɗannan yasassun wa’azozt shi ne hukumar da samar da dokar da za ta ƙayyade masu wa’azi da kuma basu lasisi. Duk wanda bashi da Lasisin wa’azi a hana shi yin wa’azi ta kowace hanya domin tsaftace al’umma daga masu zazzafar akida. Duk wanda yayi kuma hukumar farar hula su bincike shi kuma a dau kwakwaran mataki akan shi.

Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga garin Jos, kuma za a iya samun sa kan addreshinsa na yanar gizo, kamar haka; [email protected]

By ukarofi