
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Faɗar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata jita-jitar cewa akwai rikici a tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima, inda ta bayyana hakan a matsayin abinda aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.
A lokacin da ya ke magana kan batun cire sunan Shettima a yayin ayyana Tinubu a matsayin ɗan takara a tarukan APC, Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya ce babu wani rikici da hakan ke nuna akwai a tsakanin jagororin biyu.
Ya faɗi haka ne a wata hira da jaridar Daily Trust, inda ya bayyana batun a matsayin munafurci daga masu ƙoƙarin haddasa ƙiyayya tsakanin Tinubu da Shettima, yana mai cewa akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin su duba da yadda suke aiki tuƙuru wajen ciyar da Nijeriya gaba.
Ya ce, sai an ayyana ɗan takara a hukumance daga jam’iyya kafin a yi maganar zaɓar wanda zai zame masa mataimaki, saboda ba a tare ake ambatar su ba a matakin.
Onanuga ya kuma ce, irin haka ne ya faru a lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a lokacin da ya nemi tsayawa takara a karo na biyu.
Ya ƙara da cewa, da zarar Hukumar zaɓe, INEC ta fitar da jaddawalin lokacin gudanar da zaɓukan 2027, za a yi babban taron jam’iyya wanda daga nan zai zaɓi abokin tafiyarsa.
