SDP ta dakatar da shugabanta, Shehu Gabam da wasu bisa badaƙalar kuɗaɗe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jam’iyyar SDP ta sanar da dakatar da Shugabanta na Ƙasa, Shehu Gabam bisa zargin sa da hannu a sauya akalar wasu kuɗaɗen jam’iyyar.

Haka kuma, ta dakatar da Odita na ƙasa, Nnamdi Clarkson da Shugaban matasa, Chukwuma Uchechukwu.

Sakatarenta na yaɗa labarai, Araba Aiyenigba ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Talata.

Ya ce, an ɗauki matakin ne saboda samun su da hannu dumu-dumu a yin harƙallar kuɗaɗe da dama, da azurta kawunansu da sauya akalar kuɗaɗe ba tare da amincewar kwamitin ayyuka ba.

Sanarwar ta kuma ce, Shehu Gabam ya miƙa takardar bayanan kuɗaɗe da ba a amince da ita ba ga INEC da kuma wallafa ta a jaridu, lamarin da ya yi sanadin SDP ta ankara da hukumomin kuka da kiyaye doka.

Tuni aka fara gudanar da bincike mai zurfi domin haƙo baki ɗaya rahoton kuɗaɗen ayyukan jam’iyyar da kuma ƙoƙarin ɗaukar matakan shari’a akansu.

An kuma naɗa mataimakin jam’iyyar (Arewa) Sadiq Abubakar a matsayin Shugaba na riƙon ƙwarya, Kamar yadda dokokin jam’iyyar suka bayyana.

By Babaji