Rashin tabbas ya dabaibaye sulhun Iran da Isra’ila

Spread the love

Isra’ila da Iran sun amince da dakatar da faɗa a ranar Talata, bisa shawarwarin shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya bayyana cewa ƙasashen biyu sun amince da yin sulhu. Duk da haka, rahotanni sun tabbatar da cewa harin sama ya ci gaba a Isra’ila da safiyar ranar, lamarin da ya jefa sulhun cikin ruɗani da rashin tabbas.

Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya bada umarnin mayar da martani mai tsanani bisa zargin Iran da ci gaba da kai hari, duk da amincewar dakatar da faɗa. Sai dai kafafen watsa labarai na Iran sun musanta hakan, suna cewa ba su karya yarjejeniyar ba.

Sulhun ya zo ne bayan fiye da sati guda da Isra’ila ta kai hari kan Iran, lamarin da ya janyo musayar makamai masu linzami, tare da barazanar faɗaɗa yaƙi zuwa wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya da ma Amurka. Iran ta ce mutane 430 ne suka mutu a harin Isra’ila, yayin da wata ƙungiyar rajin kare haƙƙin ɗan Adam ta ce adadin ya kai 974, ciki har da sojoji 268.

A ranar Litinin, Iran ta harba makamai zuwa sansanonin sojin Amurka da ke Qatar da Iraq. Sai dai dakarun Amurka da Qatar sun daƙile harin. Shugaba Trump ya bayyana cewa Iran ta sanar da su kafin kai harin, sannan ya yi kira da kada a karya yarjejeniyar zaman lafiya. Duk da haka, har yanzu ana cikin hali na rashin tabbas kan makomar wannan sulhun.

By ukarofi