Alex na da shekara 13 lokacin da ka kammala karatu a Chicago, Atiku ga Tinubu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya fayyace dangantakarsa da wani ɗan kasuwa daga Belarus mai suna Alexander Zingman, bayan da Tinubu ya bayyana cewa shi da Alex sun yi karatu tare a Jami’ar Chicago State University (CSU). Tinubu ya yi wannan furuci ne yayin ƙaddamar da wani shiri na noma a Abuja, inda ya bayyana Alex a matsayin “maƙoci” da kuma “abokin karatu” a zamaninsa a jami’ar.

A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaran Atiku ya fitar a ranar Talata, sun ƙalubalanci ikirarin shugaban ƙasa, suna masu cewa akwai saɓani a bayanan da ke akwai a fili. Sanarwar ta nuna cewa an haifi Alexander Zingman a shekarar 1966, alhali Tinubu ya ce ya kammala jami’a a 1979. Wannan yana nufin Zingman yana da shekaru 13 kacal a lokacin da ake cewa sun yi karatu tare, wanda hakan ya sa Atiku ke tambaya ko Tinubu yana nufin Zingman ya kammala jami’a yana yaro ƙarami.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa akwai rashin tabbas da dama a tarihin karatun Shugaba Tinubu, ciki har da ƙarancin shaidu daga waɗanda suka yi karatu tare da shi a Government College Lagos da kuma CSU. Haka kuma, Atiku ya ce akwai saɓanin kwanan wata da kuma lokacin kafuwar makarantar a cikin takardun karatun da Tinubu ya miƙa, wanda hakan ke ƙara tayar da tambayoyi game da gaskiyar bayanan shugaban ƙasa.

A ƙarshe, ofishin yaɗa labaran Atiku ya jaddada cewa shugabanci ba ya buƙatar ɓoye gaskiya, yana mai kira ga shugaban ƙasa da ya fito fili ya bayyanawa ‘yan Najeriya gaskiya game da tarihin karatunsa. “Fadar Shugaban Kasa ba wurin ɓoye sirri ba ne, amma wurin gaskiya da mutunci,” in ji sanarwar. Najeriya na da haƙƙin sanin waɗanda suka shugabance ta, da kuma gaskiyar da ke bayan rayuwar su.

By ukarofi