Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi allawadai da kisan gilla da aka yi wa wasu matasa ‘yan asalin Kano guda biyu, Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad a garin Makurdi, jihar Benuwai.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an bayyana cewa wasu ɓata-gari da ba a san ko su waye ba ne suka kai wa matasan hari da misalin ƙarfe 11:00 na dare ranar Litinin, inda suka kashe su ba tare da wani dalili ba.
A cikin wani jawabi mai cike da alhini, Gwamnan ya bayyana kisan a matsayin “na rashin imani kuma abin ƙi da ƙyama.”
Ya yi tir da wannan mummunan lamari, tare da tabbatar wa jama’a cewa Gwamnatin Kano tana aiki tuƙuru don ganin an kamo masu laifin tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
“Cike da alhini da ɓacin rai ne muke sanar da rasuwar waɗannan matasa biyu ‘yan asalin Kano, waɗanda suka kasance ‘yan ƙasa nagari da ke neman halalinsu cikin kwanciyar hankali. Laifinsu kawai shi ne yin amfani da haƙƙinsu na kundin tsarin mulki don zama da aiki a wani ɓangare na ƙasar nan,” inji Gwamnan.
Gwamna Yusuf ya kuma jagoranci wata babbar tawaga, wacce za ta haɗa da iyalan mamatan, zuwa sallar jana’izar da za a gudanar a Babban Masallacin ƙasa da ke Abuja ranar Talata.
Yayin da yake jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa ‘ya’yansu, Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga fitaccen malamin addini Sheikh Ibrahim Khalil, mahaifin waɗanda aka kashe.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wannan babban rashi ba ga iyalan kawai ba ne, amma ga Kano da ma al’ummar Nijeriya baki ɗaya.
