Tinubu ya yi jimamin rasuwar Aminu Ɗantata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyarsa ta rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata, attajirin ɗankasuwa da ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a safiyar yau Asabar.

Ɗantata ya rasu ne bayan shafe shekaru 94 a duniya.

Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar hamshaƙin ɗankasuwar, wanda aka binne a Saudiyya a matsayin rashi ga Nijeriya baki ɗaya’.

Ya kuma yaba da gudunmuwar da marigayin ya bayar wajen ciyar da gaba gaba musamman a ɓangaren ilimi da kiwon lafiya.

A sanarwar da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce, “mun yi rashi na babban ɗankasuwa, mai kishin ƙasa, kuma dattijon arziƙi wanda ya ya taimaka wajen gina ƙasarmu Nijeriya.”

Tinubu ya ce, za a riƙa tuna Ɗantata a matsayin ɗankasuwa mai sanin ya kamata wanda ya bayar da gudunmuwa wajen haɗin kan ƙasa ta hanyar kasuwancinsa da ayyukan jinƙai, “wanda amfanar da ƴan Najeriya da ba za su ƙirbu ba,” kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

A ƙarshe Tinubu ya jajanta wa iyalan marigayin tare da gwamnati da al’ummar Kano baki ɗaya bisa rashin.

By Babaji