Gwamna Raɗɗa ya yi ta’aziyar rasuwar Alhaji Aminu Ɗantata

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sanarwar da ya fito daga mai magana da yawun gwamnan, Muhammad kaula gwamna Dikko Raɗɗa ya nuna kaɗuwarsa samun labarin rasuwar Ɗantata.

Ya bayyana marigayi Aminu Ɗantata a matsayin babban attajiri da babu kamar sa, wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen taimakawa al’umma.

Haka kuma malam Dikko ya ce marigayi Aminu Ɗantata sanannan ɗan kasuwa ne da ya gudanar da harkokin kasuwancin sa bama nan Nijeriya ba har zuwa wasu ƙasashe na duniya.

“Yadda marigayi ya bada gudunmawa wajen harkokin kasuwanci da taimakon al’umma a Arewacin ƙasar nan,babu shakka ya bar giɓij da za a daɗe ba a sami mai cikewa ba,”inji Dikko.

Ya ce marigayin ya tsaya akan haɓaka harkokin kasuwancin sa bane “ya maida hankali wajen taimaka wa ƙananan yan kasuwa da mabuƙata a Arewacin Nijeriya najeriya.

Gwamnan sai ya miƙa ta’aziyar sa ga gwamnati da al’ummar Jihar Kano musamman gwamna Abba Kabir Yusuf da iyalan mamacin

Yayi addu’ar Allah gafarta masa, ya yafe masa kurakuransa yasa Aljannah Firdausi ne makomar sa.

By ukarofi