Kwalejin karatun kiwon lafiya na al’umma a Funtua ta rage kuɗin rajista da kashi 50 bisa 100

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwalejin al’umma na koyon karatun kiwon lafiya da ke garin Funtua ta rage kuɗin rajista na shiga kwalejin da kashi 50/ 100 ga ɗaliban da suka fito daga makarantun da gwamnatin Katsina ta rufe.

Kwanan baya ne gwamnatin Jihar Katsina ta rufe wasu makarantun kiwon lafiya bisa gazawa na cika ƙa’idoji da dokokin da aka tanadar.

Shugaban kwalejin Dr Umar Imam ya sanar da haka biyo bayan ziyarar da ban girma da ƙungiyar haɗin kan Funtua suka kai masa a ofishin sa.

Dr Umar ya ce hukumar kwalejin ta ɗauki wannan mataki ne domin taimakawa ɗaliban da aka rufe kwalejojin ya shafa da su zo su kammala karatun su a wannan kwalejin.

Yace ya zuwa yanzu ɗalibai da aka rufe kwalejojin ya shafa guda 50 ne suka yi rajista a sashi daban daban na kwalejin.

Shugaban kwalejin ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa wannan mataki da ya ɗauka na tsarkake irin waɗannan kwalejojin kiwon lafiya a jihar.

“Nuna shakka wannan mataki da Dikko Raɗɗa ya ɗauka zai ba ɗaliban damar samun ingantaccen karatu da zasu iya aiki a kowane asibiti cikin faɗin ƙasar,”inji Dr Umar Imam.

Ya kuma yabawa Ƙungiyar haɗin kan Funtua da suka kawo masa ziyarar ban girma tare da kira da shugaban ƙungiyar kwamred Mannir Suleiman wanda tsohon malamin kiwon lafiya ne da ya rinƙa samun dama yana kawo irin wannan ziyarar domin bada shawarwari ta yadda kwalejin za ta cigaba.

A nasa jawabin shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua kwamred Mannir Suleiman ya yabawa hukumar kwalejin bisa wannan mataki na taimaka wa waɗannan ɗalibai.

“Babu shakka wannan mataki da kuka ɗauka zai taimaka wa ɗaliban su kammala karatun su ba tare da sun sami tsaiko ba,”inji kwamred Suleiman.

Ya ce wannan ƙungiyar za ta rinƙa ziyartan irin waɗannan kwalejoji da sauran manyan makarantu a faɗin jihar domin bada tasu gudunmawa wajen samar da karatu mai inganci da kuma neman hanyoyin sauƙaƙa wa ɗalibai a makarantun.

Kwamred Mannir Suleiman wanda tsohon shugaban ƙungiyar ma’aikatan kiwon lafiya a jihar Katsina ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa bisa ƙudirin sa na tsabtace karatun kiwon lafiya a jihar.

By ukarofi