Gwamnatin Tarayya za ta kori ƴan Chana 14 bisa taimaka wa ta’addanci a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Juma’a wata Babbar Kotu a Jihar Lagas ta yanke hukunci ga wasu ƴan Chana guda 14 kan samun su da laifin kitsa ta’addanci ta yanar gizo da damfara a intanet.

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta ce mutanen suna daga cikin waɗanda aka kama da manyan laifuka ta intanet a Legas bayan gudanar da wani atisaye a ranar 19 ga watan Disambar 2024.

A sanarwar da EFCC ta fitar ta kafar X, ta ce ƴan Chanan suna cikin mutane 792 da aka kama da hannu a damfara ta harkar kirifto da ƙulla alaƙa ta yaudara da ƴan Nijeriya.

An gurfanar da su ne a gaban Alƙali Daniel Osaigor bisa laifukan daban-daban da suka shafi ta’addanci da damfara ta yanar.

Ya kuma yanke musu hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan yari ko kuma biyan tarar Naira miliyan ɗaya ga kowannensu.

Sannan bayan sun kammala karɓar hukuncin, ya umarci a mayar da su ƙasar Chana acikin kwanaki bakwai ta hannun Hukumar Shige da Fice.

Sunayen masu laifiin sune Su Zong Gen, Li Zhong Chang, Chen Gui Ping, Li Xiang Long, San Feng Zhang, Jia Yang, Jia Zhi Hao, Liu Chuang, Yu Hai Ging, Zhao Xiao Liang, Dai Li, Tao Kun, Mao Bu Yi da kuma Zhao Zi Cheng.

By Babaji