Daga USMAN KAROFI a Abuja
Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar jihohi da ƙungiyoyin agaji sun saki fursunoni 7,646 daga watan Janairu 2022 zuwa Yuni 2025 a wani ƙoƙari na rage yawan cunkoso a gidajen gyaran hali na Najeriya. Rahotanni sun bayyana cewa an saki fursunonin ne ta hanyar afuwa da tallafin ƙungiyoyi masu zaman kansu da shari’o’in da manyan alƙalai suka gudanar.
A cewar alƙaluman da wakilinmu ya tattara, fursunoni 707 ne aka saki a shekarar 2022, yayin da aka saki 4,678 a 2023, sai kuma 1,843 a 2024. A farkon rabin shekarar 2025 kuwa, mutane 418 ne aka saki. Mafi yawan waɗanda aka saki sun kasance waɗanda suka gaza biyan tara da kotu ta ci su, kuma an tallafa musu da gudunmawa da ta kai Naira miliyan 585 ƙarƙashin shirye-shiryen alhakin zamantakewa.
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa wannan mataki ya taimaka wa gwamnati wajen rage kashe kuɗaɗe da ya kai kusan Naira biliyan ɗaya da ake amfani da su wajen ciyar da fursunoni. Sai dai duk da haka, matsalar cunkoso a gidajen yari na ci gaba da kasancewa babbar barazana ga tsarin gyaran hali.
Rahoton hukumar gyaran hali ta ƙasa ya nuna cewa akwai fursunoni 81,746 a halin yanzu a duk faɗin ƙasar, duk da cewa an gina gidajen ne da ƙarfin ɗaukar mutum 50,000 kawai. Daga cikin waɗannan, mutum 54,013 na jiran shari’a ne, inda da dama daga cikinsu ke fuskantar tuhume-tuhume masu tsanani irin su fashi da makami, kisa da kuma kisan gilla. Gwamnati na gina sabbin cibiyoyin gyaran hali biyu da za su iya daukar fursunoni 6,000 kowannensu a jihohin Ribas da Abuja.
