
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Shari’a Alƙali Usman na wata Kotun Shari’a dake Birnin Tudu a Ƙaramar Hukumar Gummin Jihar Zamfara ya yi nasarar tserewa daga hannun ƴan bindiga kwana ɗaya bayan garkuwa da shi.
Ƙwararren mai sharhi kan harkokin daƙile ta’addanci, Zagazola Makama ya ruwaito daga majiyoyi da dama cewa a ranar 26 ga watan Yuni ne aka yi garkuwa da Alƙalin, wanda a washe-gari, ranar Juma’a kenan da misalin ƙarfe 10 na safe ya koma gida.
Bayan haka ne aka gaggauta kai shi wani asibiti domin duba lafiyarsa, inda daga bisani aka sallame shi.
Alƙali Usman ya kuma gana da jami’an tsaron, waɗanda bayan haka suka damƙa shi a hannun iyalansa, saidai hukumomin tsaro ba su bayyana yadda ya samu damar tserewar ba.
