Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata ƙungiya a ƙarƙashin ‘Progressiɓe Youth for Greater Nasarawa’ (PYGN), ta yaba da sauye-sauyen tattalin arzikin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi, inda ta ce za su buɗe hanyoyin da Nijeriya za ta iya samun ci gaba.
Dokta Mohammed Shamsudeen, kakakin ƙungiyar ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a Lafiya gabanin ziyarar kwana ɗaya da shugaba Tinubu ya kai jihar Nasarawa.
Ya ce, ƙungiyar, wacce kuma ke goyon bayan aniyar takarar gwamna na tsohon Sufeto Janar na ’yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, ta yi imanin cewa ajandar ‘Renewed Hope’ na shugaban ƙasa ta riga ta inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.
Dokta Shamsudeen ya ƙara da cewa, ziyarar shugaban ƙasar ba wai kawai ta ƙara zaburar da shugabanci na gari ba ne, har ma za ta taimaka wajen zurfafa ci gaban ƙasa a faɗin jihar.
A cewarsa, shirin bayar da lamuni na ɗalibai na ƙasa da kuma ƙoƙarin magance ƙalubalen da ke tattare da tsarin jami’o’in ya samu goyon bayan shugaban ƙasa a tsakanin ɗaliban Nijeriya.
Shamsudeen ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa aiwatar da muhimman ayyuka a jihar Nasarawa, waɗanda wasu daga cikinsu shugaban ƙasar ya ƙaddamar a ziyarar aiki ta yini ɗaya a jihar.
A cewarsa, waɗannan ayyuka sun bayyana ƙarara na jajircewar Gwamna Sule na kawo sauyi a Jihar Nasarawa.
