Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Aƙalla ƙauyuka huɗu sun haɗu da iftila’in ambaliya sanadiyyar ruwan sama da aka yi kamar da bakin ƙwarya a ƙaramar hukumar mulki ta Arewa da ke jihar Kebbi ranar Talatar da ta gabata.
Bayanai daga yankin garuruwan Tungar Chindo, Tungar Kure, Feske Malabawa da Feske Rafi sun nuna duk da ya ke dai ba a samu salwantar rayuwa ba amma dai an tafka hasarar dukiyoyi sanadiyyar rushewar gidaje da kuma ambaliya a gonaki.
Bayanai sun nuna ambaliyar ta faru ne da sanyin safiyar Talata inda ta laƙume garin Tungar Kure bakiɗaya, Haka-zalika garin Tungar Chindo ba ginin da ke tsaye duk ruwan ya rusa.
A garin Feske Malabawa ma, sama da gidaje ashirin da biyar ne ambaliyar ta rushe, Feske Rafi ma da yawa daga cikin gidaje da shagunan garin duk sun zama kufai.
Yanzu haka dai mutanen da wannan iftila’in ya shafa suna tsugune ne a cikin azuzuwan makarantar firamare da ke Feske Rafi don samun mafaka.
Kawo yanzu dai, babu wani jami’in gwamnatin da a hukumance ya kai ziyara don jajantawa ballantana a kai musu wani agaji.
Wani magidanci Malam Abubakar Adamu ya yi kira ga hukumomin musamman waɗanda abin ya shafa da su kawo musu agaji ko da da abincin da za su ci ne saboda da yawan su, kayan da ke jikin su kadai su ka tsira da su.
Sai dai wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban karamar hukumar mulki ta Arewa Honarabul Sani Aliyu (Kulita) da danmajalisar zartaswa mai wakiltar ƙaramar hukumar mulki ta Arewa duk hakan ba ta samu ba ya kuma tura sako amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba amsar ko daya daga cikin su.
Wata mai kama da wannan haka-zalika ruwan saman ya tayarda wadansu mutane daga muhallan su a anguwar bayan kara da ke cikin garin Birnin Kebbi babban Birnin jihar ta Kebbi inda shugaban karamar hukumar mulkin Honarabul Muhammad Dahiru Nayaya Ambursa ya je ya jajenta musu ya kuma da bayarda kyautar kudi Naira dubu ɗari biyar ga wadanda abin ya shafa tare da alƙawarin kai koke ga gwamnati da kuma hukumomin da abin ya shafa don kawo musu agaji.
