Kotu ta yanke hukuncin rataya ga ɗalibin da ya kashe malaminsa a Jos

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Jihar Filato da ke zamanta a Jos, ta yanke wa dalibin nan na makarantar GSTC Bukuru, Odey Emmanuel, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe malamin makarantarsu a kan abinci.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a S.J. Bakfur, ya ce an sami Odey ne da laifin na kisan kai wanda kotun ta ce ya saba da tanade-tanaden sassa na 188 na 189 na kundin dokar manyan laifuffuka ta jihar Filato ta shekara ta 2017.

A cewar alƙalin, masu shigar da kara sun gabatar da hujjojin da suka iya gamsar da kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin da aka zarge shi da aikatawa.

Babban lauyan gwamnatin jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Philemon Audu Daffi ne ya jagoranci lauyoyi masu gabatar da kara.

Lamarin dai ya faru ne ranar 30 ga watan Yulin 2022, a cikin harabar makarantar da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.

Lauyoyin sun shaida wa kotun cewa ɗalibin ya kasha malamin ne mai suna Job Dashe a ɗakin girkin makarantyar lokacin da ake rabon abinci ga ɗalibai.

Sun ce a lokacin ne malamin a hukunta ɗalibin bisa zargin ya karɓi kason abinci har sau biyu, inda ɗalibai suka tabbatar da haka, lamarin da ya harzuka ɗalibin.

Daga nan ne ɗalibin ya dauko wuka ya daba wa malamin a kahon zuciya, nan take aka garzaya da shi asibiti amma kafin a je y ace ga garinku nan.

Sai dai ko da a aka karanta masa laifin da aka zarge shi da aikatawa a kotun, dalibin bai musa ba.

Da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun ya jaddada cewa kisan malami a makaranta babbar barazana ce ga al’umma da ya zama wajibi a dauki tsattsauran mataki a kai.

By ukarofi