An yi kira ga ɗaliban karatun allo su tashi tsaye wajen neman na kansu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Malam Abdul’aziz Mai Turawa wanda mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban majalisar Dattijai yayi wannan kira lokacin da ya ke buɗe rijiyar burtsatse da ya gina a wani masallaci da ke garin Katsina.

Ya ce wajibi ne Al’amajiri ya tashi tsaye ya nemi abin kanshi domin watarana shima ya taimaka wa al’ummar sa.

Mai Turaka ya yabawa kwamitin masallacin da suka ga ya dace su tuntuɓe shi domin ya taimakawa masallacin.

“A shirye nake in bada gudunmawa ta ba ma wannan masallacin ba, duk wani abu da ya danganci aikin Allah,” inji Mai Turaka.

Sai yayi kira ga ‘yan kwamitin da kada su gajiya wajen ƙoƙarin da suke yi na kula da masallacin da yace sakayya na gurin Allah.

Banda rijiyar burtsatse da Mai turaka ya gina ,ya kuma samar da na’urar bada wutan lantarki mai amfani da hasken rana a Masallacin.

An gudanar da addu’oi ga shi Mai Turaka da kuma addu’ar samun zaman lafiya a Jihar Katsina da ƙasa baki daya.

Mutane da dama, a ciki akwai shugaban ƙaramar hukumar Katsina Malam Ishaq Muƙidad Ɗahiru Saude da Sheikh Hadi Balarabe, suka halarci bikin da ya gudana a Masallacin da ke unguwar ɗaki tare a wakilan Kudu biyu cikin garin Katsina.

By ukarofi