Daga USMAN KAROFI a Abuja
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana mamakinsa bayan da Shugaban Liberia, Joseph Boakai, ya yi jawabi da Turanci a lokacin wata ganawa da shugabannin ƙasashen yammacin Afirka a fadar White House. Ganawar ta haɗa da shugabannin Senegal, Gabon, Guinea-Bissau, Mauritania da Liberia. Duk da cewa sauran ƙasashen suna amfani da Faransanci, Larabci da Fotugis, Liberia ce kaɗai ke da Turanci a matsayin harshen ƙasa tun daga shekarar 1822 sakamakon kafa ta da bayi da aka ‘yanta daga Amurka.
Boakai, wanda ya gabatar da jawabinsa cikin Turanci mai burgewa, ya ce: “Liberia abokiyar Amurka ce tun tuni, kuma muna goyon bayan manufofinka na mayar da Amurka babba kamar da.” Jawabin nasa ya jawo martani daga Trump wanda ya nuna mamaki da jin daɗin sa, yana cewa: “Nagode, turancinka yana da kyau matuƙa. Ina ka koya hakan? Ka yi karatu ne? A ina? A Liberia?”
Boakai ya amsa da murmushi cewa, “Eh, ranka ya daɗe.” Sai Trump ya ƙara da cewa: “Abu ne mai ban sha’awa. Turancinka yana da kyau sosai. Akwai wasu a wannan teburi da ba za su iya magana haka ba.” Wannan kalaman sun haifar da cece-kuce a kafafen yaɗa labarai da dandalin sada zumunta, inda wasu suka fassara su a matsayin nuna raini da jahilci dangane da al’adun wasu ƙasashen duniya.
Wani jami’in diflomasiya a Liberia ya bayyana wa CNN cewa kalaman Trump sun kasance “na raini kuma ba su dace ba.” A nata ɓangaren, wakiliyar majalisar dokokin Amurka, Jasmine Crockett daga jihar Texas, ta bayyana a shafin X cewa: “Wannan ne ƙololuwar jahilci.
Trump baya barin ko da damar guda don nuna wariyar launin fata da kuma kunyatar da Amurka.”
