Dalilin da ya sa na fice daga PDP zuwa ADC – Dele Momodu 

Spread the love

Daga SANI AHMAD a Abuja 

Fitaccen ɗan siyasa kuma tsohon gogaggen ɗan jaridar nan na Nijeriya, Dele Momodu ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa sabuwar haɗakar ADC ta ‘yan hamayya.

Momodu – wanda ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasar – ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yadda wasu da ya kira ”masu yaƙi da dimokraɗiyya” suka hana jam’iyyar numfashi.

Cikin wasiƙar ficewar tasa da ya aike wa shugaban jam’iyyar na mazaɓarsa ta Ihieɓbe a ƙaramar hukumar Owan ta Gabas, ranar Alhamis 17 ga watan Yuli, fitaccen ɗansiyasar ya ce dole ce ta sa ya ɗauki matakin domin maido da martabar dimokraɗiyya.

“Dalilina a bayyane yake, wasu masu yaƙi da dimokraɗiyya sun maƙure jam’iyyar daga ciki da wajen jam’iyyar,” kamar yadda wani sashe na wasiƙar ya nuna.

By ukarofi