Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya faɗa a ranar Alhamis cewa, marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi riƙo da gaskiya da adalci.
Mataimakin Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a wajen addu’o’in kwana na uku (Fidau) da aka yi na nema wa tsohon shugaban Nijeriyar gafara, a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
“Ibn Khaldun yana tunatar da mu cewa, manufar wayewa ita ce samun adalci, adalci shi ne ƙashin da ya haɗa al’ummar bil’adama. Adalci ne, kamar yadda ya fahimce shi, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bi – sau da yawa ba a fahimta ba, amma kullum cikin gaskiya.
“Lokacin da kake kan mulki abokanka sun san ka, idan ka fita daga mulki za ka san abokanka. A rasuwa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa duniya cewa shi ne babban ɗan Afirka, Allah ya ba shi rayuwarsa ta lahira, ya saka masa da Aljannah, Allah ya gafarta masa kurakuransa,” inji shi.
Mataimakin shugaban ƙasar ya miƙa godiyarsa ga Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na jihar Katsina bisa irin tarba da karamawa da aka yi wa tawagar gwamnatin tarayya a tsawon zaman da suka yi a jihar.
“Mun kasance tare da gwamnan tun daga Landan zuwa Nijeriya. Ya yi masa kyakkyawar tarba tare da dukkan goyon bayan da ya dace,” inji shi, inda ya ƙara da cewa Shugaba Bola Tinubu da kan sa ya ji zafin rashin abokinsa, ɗan uwansa da kuma abokin siyasa.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kare kima da martabar iyalan Buhari da ɗaukacin al’ummar jihar Katsina.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ce marigayin ya yi wa al’ummar ƙasa hidima, inda ya ce babu wanda zai yi jayayya da cewa shi mutum ne mai gaskiya da adalci.
Ya gode wa Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa kan karrama marigayi shugaba Buhari.
“Mu al’ummar Jihar Katsina ba mu da wata kalma da za mu gode wa Tarayyar Nijeriya, muna godiya ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya nuna tausayi da mutunta al’ummar Jihar Katsina da ma ƙasa bakiɗaya, Tinubu ya bar mambobi 25 na majalisarsa a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban ƙasa Shettima su kasance a Jihar Katsina.
“Minitoci 25 sun ba mu goyon baya a wannan mawuyacin lokaci, sannan muna kuma gode wa shugaban ƙasa da ya ayyana ranar hutu a ranar da aka yi jana’izar Buhari,” inji shi.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, ya ce marigayin yana da muhimmin matsayi a tarihin ƙasar Nijeriya, yana mai kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa tsohon shugaban addu’a Allah ya gafarta masa, kamar yadda malaman addinin Musulunci suka tunatar da su.
“Muna son miƙa godiyar ku a madadin Ministoci 25 kamar yadda mai girma Shugaban ƙasa ya umarce ku da kuka samu lokacin yin addu’o’i ga Shugaban ƙasarmu da kuma shiga wannan aiki na ƙasa baki ɗaya, haƙiƙa tsohon Shugaban ƙasa Buhari na Daura ne, Katsina, Nijeriya, da duniya baki ɗaya,” inji shi.
