Gargaɗi: Ma’aikatar Kula da Muhalli ta lissafo wuraren da ambaliya ka iya aukuwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatar Kula da Muhalli ta Ƙasa ta zayyano sunayen wasu daga cikin garuruwan da ka iya fuskantar ambaliyar ruwan sama daga ranar 16 zuwa 20 ga watan Yuli, 2025.

Ta ce, akwai yiwuwar a samu ambaliya sakamakon mamakon ruwan sama a yankunan acikin lokacin da ta bayyana.

A sanarwar da Daraktan reshen kula da lamuran ambaliya da yankunan ruwa, Usman Abdullahi Bokani ya fitar, ya lissafo wuraren kamar haka; Mubi, Jihar Adamawa; Ngala, Maiduguri a Jihar Borno; Azare, Bauchi, Itas, Jama’are, Kafin-Madaki, Jama’a, Kari da Misau a Jihar Bauchi.

Haka kuma akwai Jos, Ɓukuru da Mangu a Filato, sai Jakusko, Machina da Dapchi a Yobe da kuma Daura a Katsina.

Sauran sun haɗa da Ƙunchi, Kano, Gezawa, Wudil, Bebeji, Sumaila, Tudun Wada a Jihar Kano, sai Miga, Diginsa, Gwaram da Dutse a Jigawa da kuma Bungudu da Gusau a Jihar Zamfara.

A kudancin Nijeriya kuwa, akwai Edor, Upenekang, Oron da Eket a Akwa-Ibom sai Jihar Kuros-Riba a yankunan Kalaba da Akpap.

By Babaji