Mahara sun kashe manoma 27 a sabon hari a Filato

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

’Yan bindiga sun kashe manoma aƙalla 27 a wani sabon hari a unguwar Bindi-Jebbu da ke yankin Tahoss da ke ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato.

Maharan sun jikkata wasu da dama a yayin da aka garzaya da mamanan da kuma wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos domin ba su kulawa.

Manhaja ta samu labarin cewa waɗanda harin ya rutsa da su sun haɗa da ƙananan yara da manya maza da mata.

Jihar Filato dai a ‘yan kwanakin nan ana samun kashe-kashen rayukan al’umma, lamarin da ke da alaƙa da rikicin ƙabilanci a yankin.

By ukarofi