

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC sun zaɓi Ministan Jinƙai, Farfesa Nentawe Goshwe Yiltwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar a mataki na ƙasa.
An rantsar da shi ne da misalin ƙarfe 2:52 na rana a yayin zaman kwamitin zartarwa na APC a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja.
Sauran bayanai za su biyo baya..
